Nama ya kare a jihar Kwara sakamakon tsadar farashin shanu a yankin

Nama ya kare a jihar Kwara sakamakon tsadar farashin shanu a yankin

  • A jihar Kwara, mahauta sun koka kan yadda shanu suka kara tsada sakamakon wasu dalilai
  • Sun koka cewa, a yanzu ba sa iya yanka shanu saboda irin asarar da suke tafkawa idan suka yi
  • Sun kuma ce, ba sa iya zuwa Arewa domin sayen shanu saboda yawaitar matsalar rashin tsaro a yankunan

Kwara - Rahoto daga Daily Trust ya ce, mahauta a jihar Kwara sun daina yanka shanu sakamakon tsadar kayan masarufi.

Wannan lamarin ya haifar da karancin nama a duk kasuwanni a Ilorin, babban birnin jihar.

Wani mahauci a Kasuwar Mandate da aka fi sani da Alfa ya ce ba za su iya samun naman da za su saya daga dukkan mahautan da ke Ilorin ba.

Nama ya kare jihar Kwara sakamakon tsadar farashin shanu a yankin
Naman saniya ya kare a Kwara sakamakon tsadar shanu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wani mahauci, Abu Olowo, wanda ke gudanar da kasuwancin nama a Irewolede ya ce:

Kara karanta wannan

Abun mamaki: Bidiyo da hotunan yadda Firayim ministan Ethiopia ya koma 'direban' Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Naman ya yi tsada. Muna sayar da kilo N2,500 sabanin N1,500 da yake a da. Yanayin girman saniya, yanayin girman asaran da za a tafka kuma sabanin mu da muke siyarwa a kilo, lamarin ya fi muni ga wadanda ke cikin kasuwanni.”

Sakataren Mahautan Saraki, Akerebiata, Alhaji Oba Elegede, ya danganta lamarin da tsadar shanu.

A cewarsa:

“Kasuwar babu ita ma saboda tsadar shanu. Ta yaya za ka bayyana halin da saniya N100,000 ta koma N250,000?
“Ba za mu iya saye daga Arewa da nisa kamar Yobe da Maiduguri ba inda muke samun shanu masu arha saboda rashin tsaro. Muna zagaye kasuwannin shanu da ke kusa da Kwara, Ilesha Baruba, Kaiama, Ajase, Share, Bode Saadu, Jebba da Igbeti.
"A karshe lokacin da wasu yaran mu suka yi balaguro zuwa jihar Neja, an yi garkuwa da biyu daga cikin su kuma mun biya kudin fansa don tsira da rayukan su."

Kara karanta wannan

Ganduje, Amaechi, Ikweremadu, wasu mutum 22 da suke cin taliyar siyasa tun 1999 har yanzu

Zamu Duba Yiwuwar Kafa Dokar Hana Makiyaya Kiwon Fili a Jihar Shugaban Kasa, Gwamna

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, yace gwamnatinsa zata duba yuwuwar hana makiyaya kiwon fili a fadin jihar.

Masari ya yi wannan jawabi ne a cikin shirin 'Politics Today' na kafar watsa labarai ta Channels tv ranar Litinin.

Gwamnan ya yi watsi da yadda makiyayan suke yawo daga wannan yankin zuwa wani a fadin kasa.

Sai dai ya bayyana cewa kafin gwamnatinsa ta hana makiyaya kiwon dabbobinsu a fili, sai ta tabbatar ta samar musu wurin da zai zame musu gida, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kasurgumin shugaban 'yan bindiga ya tona asirin 'yan uwansa, ya nemi gafara

A wani labarin, Goma Samaila, shugaban gungun masu garkuwa da mutane a yankin Rigachukum ta jihar Kaduna, ya bayyana sunayen mambobin kungiyar sa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

El-Rufai zai rusa dubunnan gidaje a Garin Zaria, Gwamnati za ta tada Unguwa sukutum

Mutumin mai shekaru 47, wanda rahotanni ke cewa ya dade yana tafka ta'annuti, ya yi magana kan wasu ayyukansa da adadin kudin da ya karba a matsayin kudin fansa.

A wani faifan bidiyo, an ga Samaila yana rokon gafara yayin da daya daga cikin jami'an tsaron da ya kama shi ke tambayarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel