Gwamnan Kwara ya rusa dakin karatun da aka sanyawa sunan mahaifin Saraki
- Gwamnan jihar Kwara ya rusa wani ginin dakin karatu da aka sanya sunan mahaifin Abubakar Bukola Saraki
- Abubakar Bukola Saraki ne ya bayyana haka cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook
- Ya yi addu'ar Allah ya yalwata makwancin mahaifinsa yayin da ake rusa wani gini mai sunansa a duniya
Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ta ruguje wani ginin babban dakin karatu mai shekaru da yawa da aka sanya wa sunan mahaifin tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki.
An shirya shirin rusa dakin karatun, wanda ke kan titin Agbooba-Adeta a Ilorin, babban birnin jihar, tun ranar Juma’ar da ta gabata lokacin da aka tura jami’an tsaro yankin, inji wata majiya.
A cikin wani rubutu da Legit.ng Hausa ta samo, an ga inda Saraki ya rubuta cewa an rusa dakin karatun, kuma ya ce da umarnin gwamnan jihar ne aka yi hakan.
Saraki ya rubuta a shafinsa na Facebook a ranar Talata 28 ga watan Satumba cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na samu labarin cewa babban aikin da gwamnan jihar Kwara ya yi a yau, shine rushe wani tsohon dakin karatu na jama'a da aka sanya wa sunan mahaifina, Dakta Olusola Saraki. Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da aje wuri ga Oloye a Aljannar Firdaus."
Gbemisola Saraki, 'yar uwar Saraki, wacce ita ce karamar ministan sufuri, ita ma ta mayar da martani game da rushe dakin karatun, inji TheCable.
Ta ce:
“Har yanzu kuma, a yau mun gano cewa gwamnan jihar Kwara bai mai da hankali kan gina Kwara ba, sai dai ma rushe gine-ginen da aka mallaka ko aka sanya wa sunan marigayi mahaifina Wazirin Ilorin.
"Duk irin rushe gine-ginen da za a yi, ba za a iya lalata martabar Baba Saraki ba, saboda yana rayuwa a zukatan manyan mutanen Kwara."
Idan na yi magana kan 'yan bindiga, kawuna za su gwaru, inji Sanatan Arewa
A wani labarin, dan majalisar dattijai mai wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu, Danjuma La’ah, ya bayyana dalilan da ya sa ya zubar da hawaye a lokuta daban-daban a farfajiyar majalisa yayin da yake gabatar da kudiri kan hare-haren ‘yan bindiga a mazabarsa.
Dan majalisar na tarayya ya bayyana cewa wasu daga cikin abokan aikin sa na sanata suna tunanin ayyukan ta'addanci a Kudancin Kaduna batu ne na kudancin Kaduna kadai, SaharaReporters ta ruwaito.
Da yake magana, ya tuna lokacin da ya fada wa sanatoci cewa, akwai lokacin da dukkan mazabu 109 na sanata a kasar za su fuskanci matsala irin ta yankinsa, inda kuma ya ce yanzu hakan ya faru.
Asali: Legit.ng