Tsohon gwamnan Kwara, Abdulfatah ya magantu kan kwace gidansa da AMCON ta yi
- Tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya ce kwace gidan shi da AMCON ta yi ba tilas bane kuma tsabar azarbabi ne
- A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya a Legas ta bai wa AMCON damar kwace jerin wasu kadarorin tsohon gwamnan
- Sai dai tsohon gwamnan ya ce riga malam masallaci AMCON ta yi masa domin ya na ta kokarin tattara musu bashinsu
Kwara - Abdulfatah Ahmed, tsohon gwamnan jihar Kwara, ya ce gidan da hukumar AMCON ta kwace ba tilas ba ne kuma tsabar azarbabi ne yasa ta kwace.
Wata babbar kotun tarayya da ke Legas a ranar Laraba ta bai wa AMCON damar kwace kadarorin tsohon gwamnan kan bashin N5 biliyan da ake bin sa, TheCable ta wallafa.
AMCON ta kwatanta Ahmed da babban wanda ake bi bashi kuma wanda aka dinga bibiya amma ya ki biyan bashin, TheCable ta wallafa.
Baya ga wannan katafaren gidan shi da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara, an bai wa AMCON damar karbar wasu kadarorin tsohon gwamnan da ke fadin kasar nan.
A yayin martani ta bakin Wahab Oba, mataimakinsa a fannin yada labarai, tsohon gwamnan ya ce:
"Karbar kadarata da ke Ilorin wacce lauyan AMCON ya yi ba tilas ba ne kuma tsabar azarbabi ne saboda a halin yanzu muna tattaunawa kan lamarin."
Ahmed ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wani bashi da ya karba daga wasu bankuna biyu domin siyan hannayen jari wanda daga baya suka rushe.
Ya yi bayanin cewa, bankunan sun karba hannayen jarin domin siyarwa kuma su biya bashin wanda kawai sai aka ji batun karbe kadarorinsa.
Babu tsarin karba-karba na shugabancin kasa a kundin tsarin mulkin APC, Yahaya Bello
A wani labari na daban, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ta ce tsarin shugabancin kasa na mulkin karba-karba ba ya cikin kundin tsarin jam’iyya mai mulki ta APC.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin taron nada shugaban wata kungiyar matasan arewa a Kaduna inda ya ce matasan Najeriya ne suke da alhakin zaben shugaban kasa.
Daily Trust ta ruwaito yadda rantsarwar kungiyar da suke kira YBN ta kasance wanda bai kai kwana 3 ba da kungiyar dattawan arewa ta NEF ta ce akwai yuwuwar arewa ta ci nasarar zaben 2023 saboda ta na da yawan da za ta iya cin zaben shugaban kasa.
Asali: Legit.ng