Labaran garkuwa da mutane
Masu garkuwa da mutane sun tafka sabuwar ta'asa da rashin imani a birnin tarayya Abuja. Miyagun mutanen dai sun halaka mutum hudu da suka yi garkuwa da su.
Dan takarar shugaban kasa a Labour ya bayyana kadan daga tashin hankalin da ya shiga bayan samun labarin kisan da aka yiwa Nabeeha bayan sace su da aka yi.
Sherifdeen Al-Kadriyar, kawun Nabeeha yarinyar da yan bindiga suka kashe bayan sun yi garkuwa da ita da yan uwanta ya bayyana yadda suka gano gawarta a wani wuri.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe wata Nabeeha Al-Kadriyar, daya daga cikin mata shida 'yan gida daya da suka yi garkuwa da su a birnin tarayya Abuja
‘Yan bindiga sun sake yin garkuwa da wani malamin jami'ar tarayya da ke Gusau, jihar Zamfara, bayan da suka kutsa gidansa a safiyar ranar Laraba.
Kimanin mutane 85 ne ‘yan bindiga suka sace a jihar Kaduna a hare-haren da aka kwashe kwanaki hudu ana kai musu. 'Yan sanda sun mayar da martani.
Bayan sama da watanni 10, yan bindiga sun dawo da ayyukansu a kan babban titin Kaduna zuwa Abuja, sun yi garkuwa da mutane 30 a ranar Lahadi, 7 ga watan Janairu.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sanye da kayan Fulani sun kai hari Sagwari da ke Abuja, sun sace mutum 10. Sun kai harin karfe 7:30 na yammacin ranar Lahadi,
Wasu miyagun yan bindiga sun halaka magajin garin Wuro Musa da suka sace a jihar Taraba ranar Jumu'a. An kashe manomi tare da sace wasu kauyukan Kaduna.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari