Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Jihar Kwara, Sun Sace Mutane da Yawa

Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Jihar Kwara, Sun Sace Mutane da Yawa

  • 'Yan bindiga sun kai hari garin Ora da ke yankin ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, sun yi garkuwa da mutane da dama
  • Yayin wannan harin, an ce maharan sun shiga fadar basaraken yankin, Oba C.O Odeyemi, sun tafka ɓarna kuma sun kwashi kaya
  • Shugaban ƙaramar hukumar ya ce tuni aka bai wa yan banga kayan aiki domin su bi sawun maharan da nufin ceto mutanen

Jihar Kwara - Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki garin Ora da ke yankin Ayetoro a karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, inda suka yi garkuwa da wasu mazauna garin.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata inda ‘yan bindiga kimanin tara, hudu daga cikinsu sanye da abin rufe fuska, suka far wa garin dauke da bindigogi kirar AK-47.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban Karamar Hukuma da Wasu Mutane 12 a Jihar Arewa

Yan bindiga sun sake kai hari a jihar Kwara.
Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Jihar Kwara, Sun Sace Mutane da Yawa Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Yan bindigan sun tafka ɓarna a fadar Sarki

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun kutsa kai cikin fadar basaraken yankin, Oba C.O Odeyemi, sun tafka ɓarna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin ta'asar da suka tafka a fadar Sarkin, maharan sun lalata gidansa kana suka fasa shagon matarsa, Olori Odeyemi, suka kwashi kayayyaki da tsabar kuɗi.

Shugaban karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara, Mista Kayode Bayode, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar.

Wane mataki mahukunta suka ɗauka?

A cewarsa, an baiwa ‘yan banga na yankin damar yin aiki tare da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin ceto wadanda lamarin ya shafa, Tribune ta tattaro.

Ciyaman din ya ce:

“Sun lalata fadar sarkin mu tare da wawushe kaya irinsu indomie, taliya da sauran kayayyaki da tsabar kudi a shagon matarsa ​​saboda ba su kusa."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Kwantan Ɓauna, Sun Kai Hari Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Arewa

“A yanzu da muke magana a daren nan, mutanen mu na can sun bi sawun maharan duk da ruwan sama na sauka yanzu."
"A nawa bangaren na samar da bindigu guda uku ga ’yan banga tare da harsasai domin samun damar tunkarar masu garkuwa da mutane. Ina da yaƙinin zasu ceto su zuwa gobe (Jumu'a)."

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Ajayi Okasanmi SP, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce:

"An tura Jami'an tsaro tare da 'yan banga da mafarauta zuwa cikin daji domin su ceto wadanda yan bindigan suka tafi da su."

Shugaban Nijar da Aka Hamɓarar Ya Yi Yunkurin Tserewa Daga Hannun Sojoji

A wani labarin kuma Mohammed Bazoum, shugaban Jamhuriyar Nijar da aka hamɓarar ya yi yunkurin tserewa daga hannun sojoji.

Kakakin gwamnatim soji, Amadou Abdramane ne ya bayyana haka yana mai cewa an dakile shirin kuma an kama masu hannu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Gidan Yari a Najeriya, Sun Kashe Jami'in Tsaro

Asali: Legit.ng

Online view pixel