Yan Bindiga Sun Sace Mutane da Yawa a Ƙaramar Hukumar Jihar Kano

Yan Bindiga Sun Sace Mutane da Yawa a Ƙaramar Hukumar Jihar Kano

  • 'Yan bindiga sun kashe mutane sun yi garkuwa da wasu da ba a tantance yawansu ba a karamar hukumar Ƙaraye ta jihar Kano
  • Mazauna ƙauyuna Yola da abun ya faru sun ce maharan sun kai hari a jere, sun tafka ta'asa tun daga ranar Asabar da ta wuce
  • Ƙaraye da Rogo na fuskantar barazanar hare-haren 'yan bindiga saboda kusancin Rogo da jihohin Kaduna da Katsina

Kano - Rahotanni sun bayyana cewa har yanzun ba a tantance yawan mutanen da yan bindiga suka sace da waɗanda suka kashe ba a ƙauyen Yola, ƙaramar hukumar Ƙaraye a jihar Kano.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, hakan ya faru ne bayan jerin hare-haren da 'yan bindigar suka kai ƙauyen a baya-bayan nan.

Yan bindiga sun shiga Kano sun sace mutane.
Yan Bindiga Sun Sace Mutane da Yawa a Ƙaramar Hukumar Jihar Kano Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wani mazaunin garin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda tsaro ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar a lokuta daban-daban a kauyen.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an Tsaron Haɗin Gwiwa Sun Yi Artabu da Makiyaya, Ana Fargabar da Yawa Sun Mutu

Ya bayyana cewa ba zai iya tantance yawan mutanen da aka sace ko aka kashe ba yayin harin. Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Na samu labarin cewa a harin farko da aka kai, an yi garkuwa da mutane kusan hudu, aka kashe biyu yayin da a hari na biyu an sace mutane biyu sannan aka kashe daya."
"A zahirin gaskiya yanzun ƙaraye na buƙatar a girke mata dakarun sojoji saboda irin waɗan nan hare-hare."

Kananan hukumomi 2 a Kano na fuskantar barazana

An tattaro cewa a baya-bayan nan, yankin kananan hukumomin Karaye da Rogo na Kano na fuskantar barazanar rashin tsaro saboda kusancin Rogo da jihohin Katsina da Kaduna.

An ce a watan Afrilun 2023, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani shahararren dan kasuwa a kauyen Gangarbi da ke karamar hukumar Rogo ta Jihar Kano, Alhaji Nasiru Na’ayya, tare da kashe mutum daya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mata Sama da 25 da Kananan Yara a Jihar Arewa

Haka nan a 2021, Masarautar Ƙaraye ta ankarar da cewa masu haƙar ma'adanan Zamfara ba bisa ƙa'ida sun fara shigowa yankin, kuma ta bada shawarin yadda za a magance matsalar.

Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ci tura domin bai amsa kiran da aka yi masa ba.

Yan Sanda Sun Ceto Mutane 171 da Aka Yi Garkuwa Da Su a Jihar Katsina

A wani rahoton kuma Dakarun rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun sheƙe yan bindiga huɗu, sun ceto mutane sama da 170 da aka yi garkuwa da su.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ' yan sanda reshen Katsina , ASP Abubakar Aliyu, shi ya bayyana haka ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262