Labaran garkuwa da mutane
‘Yan bindiga za su hallaka daliban jami’ar Gusau da aka yi garkuwa da su. Nan da mako guda za a kashe daliban idan ba a fito da mutanensu da ke tsare ba.
Masu garkuwa da mutane sun sace tsohon ciyaman na karamar hukumar Yorro, Hon. Ishaya Dimas Dila, tare da wasu mutum 10 a kauyen Dila da Kunini, a ranar Lahadi.
Bayan makonni uku da yin garkuwa da shi tare da wasu da dama, 'yan bindiga sun kashe malamin kwalejin ilimi ta jihar Zamfara bayan karbar naira miliyan biyu.
Masu garkuwa da mutane sun sace wani mawaki da masu masa kida a hanyar Abuja zuwa Kogi. Yan bindigar na neman nara miliyan 10 kudin fansar duk mutum daya.
Shugaban jami'ar FUDMA, Farfesa Armaya’u Hamisu-Bichi, ya sanar da cewa ragowar ɗalibai mata hudu da ke hannun yan bindiga sun shaki iskar yanci.
Yan bindiga sun shiga garin Zurmi, hedkwatar ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, ana fargabar sun sace mutane 10 ciki har da mai jego da jaririnta.
Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 12 a kauyen Gbaupe da ke ƙarƙashin birnin tarayya Abuja ranar Lahadi, sun kuma kashe jami'in yan banga ɗaya.
Wasu tsagerun yan bindiga sun shiga kauyen Unguwar Liman a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, sun sace mutane harda mata da kananan yara masu yawa.
An kai hari a Gidan Shaho washegari aka koma kauyen Nasarawar Zurmi inda aka yi asarar mutane, rayuka, dukiya da abinci. Yanzu Mutane sun tsere da suka koma Zamfara
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari