Labaran garkuwa da mutane
Yan bindiga sun kai hari jihohin Zamfara da Katsina inda suka kashe mutane kimanin 50. Kwamishinan yan sandan jihar Zamfara ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yadda wasu direbobin kasar nan ke awon gaba da wasu jami'an tsaro idan an tsare su a hanya ya fara ci wa rundunar 'yan sandan kasar nan tuwo a kwarya.
Rundunar yan sandan Kano ta cafke wasu mutane 19 da ake zargi da aikata mugayen laifuka iri daban-daban a jihar, ciki har da fashi da makami da satar mutane.
Gwamnatin jihar Niger ta dora laifin gaza ceto wadanda suka makale a karkashin mahakar ma'adanai kan rashin tsaro da ya addabi yankin Galadima-Kogo.
Wasu yan ta'adda sun shiga kauyuka biyu a kananan hukumomin Nunya da Tunga, sun yi awon gaba da Bayin Allah akalla 56 a jihar Neja cikin kwanaki biyu.
Rindunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa dakarun soji sun ragargaji ƴan ta'adda a wani samame da suka kai maɓoyarsu a jihar Benuwai, sun kuɓutar da mutane da dama.
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kashe yan bindiga uku a jihar Benue. Ta ce ta samu kubutar da jami'an soji da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.
Rundunar sojin Nijar ta sanar da kwamushe kasurgumin dan ta'addan Najeriya da ake kira Baleri wanda shi ne mai gidan babban dan bindiga Bello Turji.
Rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta samu nasarar damke wata mata mai shekaru 21 da jaririn da ta sato wanda tuni ta shaidawa mutane cewa ita ce ta haihu.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari