Labaran garkuwa da mutane
Sojojin Najeriya sun kama yan bindiga a Wukari da Ibi a jihar Taraba, yan bindigar sun ba sojojin cin hancin N2m domin a sake su amma sojojin sun ki yarda.
Yan bindiga sun shiga kauyen Dawaki a kusa da Bwari a Abuja, sun ɗauki mutane da dama amma ƴan sanda sun kai ɗauki kuma ana tsammanin sun ceto mutanen.
Yan bindiga sun kai hari anguwar Shagari da ke Dei- Dei a birnin tarayya Abuja tare da yin garkuwa da jami'in kwastam da matarsa da 'ya'yansa guda uku.
Wata kungiya a jihar Neja ta bayyana halin da matan da yan bindiga suka kashe mazajensu suka shiga a kauyuka sama da 80 a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Yan sandar Najeriya sun kama gungun masu garkuwa da mutane a jihar Delta. Cikin mutane ukun da aka kama daya ya ce ya zo Najeriya ne daga kasar waje.
Tsagerun ƴan bindiga sake kai hari kauyen Yar Malamai jim kaɗan bayan jami'an tsaro sun tashi, sun sace mutane da yawa tare da tafka ɓarna ranar Litinin.
Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya ya koka kan yadda matsalar rashin tsaro ta cigaba a yankin Arewa. Ya ce matsalar za ta iya shafan Afirka ta yamma
Kwamishinan 'yan sandan jihar Edo ya bada umurmi ga jami'ansa kan yin hadaka da yan banga wurin ceto ma'aikatan kamfanin simintin Dangote da aka sace.
Dan majalisar Zurmi da Shinkafa ya bayyana cewa al'ummar kauyuka 50 a yankin Zurmi sun gudu sun bar gidajensu saboda yawan hare-haren ƴan bindiga a kwanan nan.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari