Kasashen Duniya
Uku daga cikin manyan sojojin da suka taimaka wajen kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a jihar Jamhuriyar Nijar, an ba su muƙamin ministoci a ƙasar.
Masu binciken lafiya sun fadi cewa taku 4,000 a ko wace rana na rage saurin mutuwa da kuma kara lafiyar zuciya, binciken ya ce dattawa na bukatar taku 10,000.
Ɗan takarar shugaban ƙasar Ecuador, Fernando Villavicencio, ya gamu da ajalinsa bayan an buɗe masa wuta a wajen wani gangamin taron yaƙin neman zaɓe a ƙasar.
A yau Sarkin Kano na 14, kuma Halifan darikar Tijjaniyyah na Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya samu ganawa da Shugaban mulkin sojan Nijar, Abdulrahmane Tchiani.
Ibraheem El-Zakzaky ya bayyana cewa kusan jirgi daya ya dauko mutanen Nijar da na Najeriya, ya ja-kunne a kan shirin aukawa makwabta da yaki da sunan ECOWAS.
Gwamnatin sojoji da Janar Abdourahamane yake jagoranta a Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarnin kulle sararin samaniyar kasar bisa tsoron mamayar da za a kawo.
Sheikh Bello Yabo ya gargadi Gwamnati cewa mutanen Nijar da Najeriya ‘yanuwa ne, Malamin Musulunci ya caccaki shugaba Tinubu a kan shirin yaki da makwabtan.
Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Abdulsalami Abubakar ya jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Nijar don tattaunawa da shawo kan matsalar kasar bayan juyin mulki
Wani matashi ya tsere daga gidan kaso watanni hudu kafin wa'adinsa, an sake kama shi ya na aikata laifuka tare da yanke masa hukuncin shekaru 40 a gidan kaso.
Kasashen Duniya
Samu kari