Za Mu Ce Majalisa ta Tsige Tinubu Idan Ya Turawa Nijar Sojojin Yaƙi - Sheikh Bello Yabo

Za Mu Ce Majalisa ta Tsige Tinubu Idan Ya Turawa Nijar Sojojin Yaƙi - Sheikh Bello Yabo

  • Bello Yabo ba ya goyon bayan Sojoji su shiga Nijar da nufin dawo da Mohammed Bazoum kan mulki
  • Malamin addinin ya na ganin abin da Najeriya za ta iya yi shi ne a bada shawara ba amfani da karfi ba
  • Sheikh Yabo ya gargadi Gwamnatin Bola Tinubu da cewa mutanen Nijar da Najeriya ‘yanuwa ne

Sokoto - Malamin addinin muuslunci, Muhammadu Bello Yabo, ya tofa albarkacin bakinsa a kan abin da yake faruwa bayan juyin mulki a kasar Nijar.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin karatun malaman Sunnah, Sheikh Bello Yabo ya yi tir da zargin yunkurin aukawa sojojin Nijar da yaki da ake yi.

Malamin ya zargi sabuwar gwamnatin Najeriya da rashin mafadi, ya ce idan mulkin farar hula na jama’a ne, to su ba su goyon bayan a aukawa Nijar.

Kara karanta wannan

Mun fi karfinku: Jigon APC ya gargadi sojojin Mali, Nijar da suke barazanar taran na Najeriya

Bola Tinubu
Bello Yabo ya soki Bola Tinubu a kan Nijar Hoto: Ajuri Ngelale & Ahmed Mohammed
Asali: Twitter

Iyakar na mu shi ne shawara

Bello Yabo yake cewa abin da ya dace Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi shi ne ya ba Nijar da mutanenta shawarwa, ba kokarin auka masu da yaki ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wajen babban malamin addinin musuluncin, babu bambanci tsakanin Nijar da Najeriya, ya ce musamman ‘Yan Arewa da tamkar ‘yanuwa juna ne.

Yabo yake cewa jirgi daya ya dauko Fulani, Hausawa, Zabarmawa, Buzaye da ke yankin nahiyar. Ba wannan ne karon farko da aka gargadi kasar ba.

Muddin dakarun ECOMOG su ka shiga Nijar da nufin dawo da farar hula, Sheikh Yabo ya ce an kama hanyar yanke zumuncin da yake tsakanin kasashen.

Yabo: "Nijar da Najeriya 'yanuwa ne"

"Ba hakkinsa ba ne, Allah ba zai tambaye shi game da harkar kasar Nijar ba. Juyin mulki maganar cikin gidan Nijar ne ba na mu ba.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Dalilin Da Ya Sanya Yakamata Najeriya Ta Sake Dawo Da Doka Da Oda a Nijar, Reno Omokri Ya Bayyana

Babu bambanci tsakanin Nijar da Sokoto, duk ‘yanuwanmu ne. Ba mu su son a kashe kowa, ko da kaza. Mutanen Nijar Musulmai ne."

-Muhammad Bello Yabo

Har ta kai an ji malamin yana cewa za su nemi ‘yan majalisa su tsige Bola Tinubu idan ya dage a kan jagorantar runduna domin a yaki Nijarawan.

Shawara ga sojojin Najeriya

Da yake karatun hadisi a karshen makon jiya, shehin ya ce idan Najeriya ta na takama da soji, ta ceto mutanenta da ‘yan bindiga ke garkuwa da su.

Idan yaki ya barke, Bello Yabo ya ce za ayi asarar rayuka musamman na musulmai a yankin, saboda haka ya yabawa matsayar Sanatocin jihohin Arewa.

Y/Afrika ta na tsaka mai wuya

A wani rahoto, kun fahimci cewa idan kungiyar ECOWAS ta zura ido kan lamarin Nijar, ‘Yan ta’adda za su iya sake mamaye Najeriya ta makwantanta.

A gefe guda kuma amfani da karfi zai iya jawo kasashen Afrika su shiga yaki, su yi ta kashe junansu bayan hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel