Kasashen Duniya
Dubun wasu gungun Mata 3 yan Najeriya dake sana’ar fashi da makami a kasar Dubai ta cika bayan sun yi ma wani attajirin balarabe dan asalin kasar Iraqi fashi da makamin kudinsa Dh57,000.
Wata mata dake zaune a birnin Georgia dake kasar Amurka an ruwaito cewa ta kashe 'ya'yanta guda biyu sannan ta juya bakin bindigar da tayi amfani da ita wajen kashesu ta kashe kanta. A cewar rahoton, matar mai suna Marsha Edwards.
Wani Lauya mai shigar da kara a kotu ya roki Birtaniyya ta fatattako Jagoran Biyafara, Nnamdi Kanu ya dawo gida Najeriya. Lauyan ya taso Gwamnati a gaba ta sa a maido Nnamdi Kanu inda a ke shari’a da shi.
Fitaccen attajirin nan da ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika, yayi bayanin cewa bashi da gida ko guda daya a wata kasa wacce ba Najeriya ba. Da yake bayani a wajen taron gidauniyar 'Mo Ibrahim' na wannan shekarar ta 2019...
Hare-haren da suka auku a kauyuka biyu na gundumar Marsabit da ke kan iyaka da kasar Habasha, sun kasance masu kiwon shanu 'yan kabilar Gabra wanda adawa ta tsawon shekaru aru-aru ke tsakaninsu da kabilar Borana.
Mace za ta cigaba da zama a gidan iyayenta koda kuwa ta yi aure, sai dai mijin da ta aura yake kawo mata ziyara, kuma mace ce keda ikon zabin mijin da take son aura. Sai dai, gabatar da shari'ar Musulunci a yankin da kabilar Mina
A cikin sanarwar da Bashir ya fitar, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Yokohama na kasar Japan domin wani halartar wani taro da za a yi a ranar Laraba, 28 ga watan Agusta, 2019. Za a yi taron ne a kan cigaban
Sannan ya cigaba da cewa, "amma mutane da dama, musamman matasa, na son rayuwar jin dadi. Babban kalubalen da mutanen Afrika ke fuskanta shine kashe kudinsu tun kafin ya shigo hannunsu." "Yawancin masu kasuwanci na yin wani kuskur
Da sanadin kafar watsa labarai ta BBC Hausa mun samu rahoton cewa, a yayin da wata cuta da ake kira ANCA Positive Vasculutis, ta addabi wata mata a kasar Ingila, Jayne Hardman, ta sanya an sauya mata karan hanci da kofofinsa.
Kasashen Duniya
Samu kari