Lauya ya taso Kasar Ingila a gaba ta sa a maido Nnamdi Kanu gida

Lauya ya taso Kasar Ingila a gaba ta sa a maido Nnamdi Kanu gida

Wani Lauya mai shigar da kara, Donald Okonkwo, a wata sabuwar shari’a da ya shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja, ya nemi ofishin Jakadancin Birtaniyya ta dawo da Nnamdi Kanu gida.

Donald Okonkwo ya na so ofishin Jakadancin na Turai ya fatattako jagoran na kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, mai fafutukar neman kasar Biyafara mai cin-gashin kan ta da ya dawo Najeriya.

Lauyan ya shigar da wannan kara ne a Ranar Litinin, 27 ga Watan Agusta, 2019. Wannan Lauyan ya hada da Jakadancin kasar Ingila da Ministan shari’a da kuma Darektan DSS a wannan kara.

A wannan kara da Lauyan ya shigar, ya kafa hujja a dawo da Nnamdi Kanu saboda hare-haren da wannan kungiya ta sa ta IPOB ta ke kai wa mutane wanda ba sa san hawa ba, ba su san sauka ba.

Daga cikin wadanda IPOB ta kai wa hari akwai irin su babban Sanata Ike Ekweremadu a kasar Jamus. Sannan kuma kungiyar ta fara barazanar damke shugaban Najeriya Buhari a kasar Jafan.

KU KARANTA: Kotu ta bada belin wadanda a ke tuhuma da laifi sata a kamfanin Dangote

Donald Okonkwo ya nemi a yi la’akari da wannan tabargaza na Mazi Nnamdi Kanu a cafke shi a dawo da shi Najeriya. Okonkwo ya ce asali ma hukuma ta haramta kungiyar Kanu ta IPOB.

Lauyan ya na so kotu ta umarci Jakadancin Birtaniya ta ba gwamnatin tarayyar Najeriya hakuri a fili a gidajen jaridu uku cikin kwana 21 game da sakacin da kasar ta yi wajen tserewar Kanu.

Okonkwo ya fadawa kotu cewa daga bada belin Mazi Nnamdi Kanu ne kurum sai a ka ji labarinsa a kasar Israila a 2018. Daga baya kuma a ka gan shi a cikin kasar Ingila inda ya ke gujewa shari’a.

Wannan Lauya ya na zargin kasar wajen da shiryawa Nnamdi Kanu yadda zai tsere daga shari’ar da a ke yi da shi a Najeriya na cin amanar kasa. Ba mu samu labarin yaushe kotu za ta zauna ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel