Ma'aikata na sun sayi gidaje a kasar Ingila, amma bani da gida a wata kasar waje - Aliko Dangote
Aliko Dangote, fitaccen attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika, ya bayyana cewa bashi da wani gida a wata kasa bayan Najeriya.
Da yake magana a wurin taron gidauniyar 'Mo Ibrahim' na shekarar 2019, hamsahakin dan kasuwar ya bayyana cewa ba rayuwar wacaka da dukiya yake yi ba, "bana amfani da abubuwa masu tsada saboda zasu dauke min hankali kuma su ci min lokaci"
"Ba ni da wani gidan huta wa a ko ina. Ba ni da gida a ko ina bayan Najeriya amma na san mutanen da ke min aiki da suke da gidaje a birnin Landan", a cewarsa.
Sannan ya cigaba da cewa, "amma mutane da dama, musamman matasa, na son rayuwar jin dadi. Babban kalubalen da mutanen Afrika ke fuskanta shine kashe kudinsu tun kafin ya shigo hannunsu."
DUBA WANNAN: Kaftin Tijjani Balarabe: Ku sadu da jami'in sojan da ya jagoranci kubutar da Wadume daga hannun 'yan sanda
"Yawancin masu kasuwanci na yin wani kuskure daya; da zarar mutum ya fara kasuwanci yana samun riba, sabanin ya kara fadada kasuwancinsa ko neman kudi, sai kawai ya fara kashe kudi bisa tunanin cewa riba zata cigaba da zuwa," a cewar Dangote.
Kazalika, ya bayyana cewa, "akwai canje-canje da kalubale masu yawa a cikin kasuwanci, akwai bukatar dan kasuwa ya kasance mai matukar lissafi."
Da yake amsa tambaya a kan bangaren kasuwanci da zai bawa matasa shawarar su runguma, sai Dangote ya amsa da cewa: "bangaren kasuwanci da duniya ke dama wa da su a yanzu su ne fasahar sarrafa bayanai ta zamani (ICT) da kuma noma."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng