An haramtawa ma'aikatan gwamnati buga waya a Senegal

An haramtawa ma'aikatan gwamnati buga waya a Senegal

A wani sabon tsari da gwamnatin kasar Senegal ta kawo na tsimi gami da tattalin kudi, za ta haramtawa manyan ma'aikatan gwamnati buga waya da zummar rage kashe-kashen kudaden gwamnati.

BBC Hausa ta ruwaito cewa, gwamnatin Senegal za ta sanya wa ministoci da kuma ma'aikatansu takunkumi na yadda ba za su samu damar buga waya ba sai dai su amsa kira a yayin da aka kira su daga yanzu zuwa karshen watan Sataumban da muke ciki.

A rahoton da muka samu daga kamfanin mai dillancin labarai, ba dukkanin ma'aikatan gwamnati wannan mataki zai shafa ba, lamarin da gwamnatin kasar ta ce ba zai shafi jami'an tsaro ba da kuma ministocin harkokin cikin gida.

Gwamnatin Senegal dai ta ce wannan yunkuri zai ba ta damar tsimi da tattalin wasu kudade wanda za ta ribata a wasu bangarori na inganta jin dadin al'umma musamman harkokin kula da lafiya da ilimi da makamantansu.

Cikin wani jawabi mai kunshe a sanarwar da ya gabatar kan sake tsarin ma'aikatun gwamnatin kasar, Shugaba Macky Sall, ya ce tun yayin hawansa kujerar mulki a shekarar 2012, gwamnatin sa ta batar da Dalar Amurka miliyan 28 wajen ta'ammali da wayoyin sadarwa a ma'aikatun gwamnati.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta shiga zaman sulhu kan rikicin kabilanci na jihar Benuwe da Taraba

Hakazalika shugaban kasar ya ce a tsawon shekaru bakwai da ya shafe a bisa kujerar mulki, an kashe dala miliyan 518 wajen sayen motoci a ma'aikatun gwamnati, lamarin da ya ce dole gwamnatinsa ta bijiro da wasu hanyoyi na rage kashe-kashen kudi.

Ana iya tuna cewa, a farkon shekarar da muke ciki ne, shugaba Macky Sall, ya soke wasu mukamai na firaiminista da na wasu ministocin kasar domin rage kashe-kashen kudaden gwamnati.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel