Barayin shanu sun kashe mutum 12 a Kenya
Akalla mutane 12 da suka hadar da kananan yara uku aka kashe a wasu munanan hare-hare guda biyu da suka auku a Arewacin kasar Kenya a karshen makon da ya gabata.
Hukumar 'yan sandan kasar a ranar Lahadi ta ce barayin shanu da ake zargi sun fito daga kabilar Borana ke da hannu a wannan mummunar ta'asa.
Hare-haren sun auku a kauyuka biyu na gundumar Marsabit da ke kan iyaka da kasar Habasha, a yayin da suka kasance masu kiwon shanu 'yan kabilar Gabra wanda adawa ta tsawon shekaru aru-aru ke tsakaninsu da 'yan kabilar Borana.
Rayukan maza biyar 'yan kabilar Gabra sun salwanta yayin da wasu uku suka jikkata da Yammacin ranar Asabar kamar yadda hukumar 'yan sandan kasar ta bayar da shaida.
Ana zargin maharan da suka yi awon gaba da garke guda na shanu kimanin 500 sun kasance 'yan kabilar Borana da suka hauro daga kasar Habasha.
KARANTA KUMA: Ikogho: Mutumin da FBI ta damke a Amurka aminina ne tun muna yara - Festus Keyamo
A daya harin kuma da ya auku a wani kauye na kurkusa, rayukan maza 4 da kuma na yara 3 masu shekarun samartaka da suka hadar da mace daya sun salwanta a yayin da mutane hudu suka jikkata.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, maharan sun yi awon gaba da kimanin awakai 1000 a yayin zartar da harin na biyu inda aka samu nasarar kashe daya daga cikin masu ta'adar.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng