Mata 3 yan Najeriya sun yi ma wani attajirin balarabe fashi da makami a Dubai

Mata 3 yan Najeriya sun yi ma wani attajirin balarabe fashi da makami a Dubai

Dubun wasu gungun Mata 3 yan Najeriya dake sana’ar fashi da makami a kasar Dubai ta cika bayan sun yi ma wani attajirin balarabe dan asalin kasar Iraqi fashi da makamin kudinsa Dh57,000.

Jaridar The Cable ta ruwaito matan da ba’a bayyana sunayensu ba, amma shekarunsu 30, 33 da 34 sun lakada ma balaraben nan dan banzan duka, sa’annan suka rabashi da makudan kudade da suka yi daidai da N5,625,127.69.

KU KARANTA: Najeriya ta tura matasa 60 kasar China don koyon yadda ake hada na’urar raba wutar lantarki

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yanzu haka an gurfanar da yan fashin gaban kotu, kuma ana sa ran yanke musu hukunci zuwa karshen wannan wata na Agusta.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa balaraben Iraqin mai shekara 45 ya shiga Dubai ne a watan Janairu inda ya hadu da wata budurwa da yake tsammanin yar kasar Sweden ce, ta wani manhajar abota.

Amma isarsa dakin matar dake wani gida a yankin Al-Qouz na kasar Dubai keda wuya, sai ya tarar da wasu gungun mata guda 5 yan Afirka da suka far masa, suka casa shi, sa’annan suka nemi ya basu kudin dake hannunsa.

“A nan na basu Dh1,600 domin su kyaleni na tafi, amma basu yarda ba, sai da suka caje aljihuna suka gano Gh55,975, ganin wannan kudi ya faranta musu rai, amma duk da haka na ji tsoron kada su kasheni sai na fara yi kamar numfashina ya dauke, ganin haka yasa suka kyaleni na tafi.

“Ina fita na sanar da jami’an tsaron Otal din, nan da nan suka shaida ma Yansanda, yayin da muka tsare kofar shiga Otal din ko za su fito ta nan, ashe sun haura ta taga ne, koda Yansanda suka iso, sai muka bi su da gudu a kafa, da kyar muka kama guda 3.” Inji shi.

Sai dai shima Balaraben bai sha ba, sakamakon hukumomin Dubai sun zargeshi da neman karuwai, don haka aka cajeshi Dh5,000, sa’annan aka mayar dashi kasar Iraqi da karfi da yaji.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel