Mai kudi ma kenan, bare talaka: Bani da gida ko daya a kasar waje, saboda bana rayuwa mai tsada - Aliko Dangote
- Hamshakin mai kudi na nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa ba shi da gida ko guda daya a kasar waje
- Ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da ya halarta na bude wata gidauniya mai suna 'Mo Ibrahim'
- Dangote ya bayyana cewa shi baya rayuwa mai tsada ko kadan, saboda ya san cewa za ta dauke hankalinshi daga kan abubuwan da yake yi
Fitaccen attajirin nan da ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika, yayi bayanin cewa bashi da gida ko guda daya a wata kasa wacce ba Najeriya ba.
Da yake bayani a wajen taron gidauniyar 'Mo Ibrahim' na wannan shekarar ta 2019, shahararren dan kasuwar ya bayyana cewa shi ba rayuwa yake yi wacce take da tsada ba, "Bana amfani da abubuwa masu tsada saboda na san zasu dauke mini hankali su kuma cinye mini lokaci."
"Ba ni da wani gidan hutu ko ina a duniya, ba ni kuma da gida a kasar da ta wuce Najeriya, amma kuma na san yarana da suke yi mini aiki da suke da gidaje a birnin Landan," a cewarsa.
KU KARANTA: Kyawawan hotunan 'yan matan Kannywood guda takwas da har yanzu ba su yi aure ba
Sannan ya cigaba da cewa, “amma mutane da dama, musamman matasa, na son rayuwar jin dadi. Babban kalubalen da mutanen Afrika ke fuskanta shine kashe kudinsu tun kafin ya shigo hannunsu.”
“Yawancin masu kasuwanci na yin wani kuskure daya; da zarar mutum ya fara kasuwanci yana samun riba, sabanin ya kara fadada kasuwancinsa ko neman kudi, sai kawai ya fara kashe kudi bisa tunanin cewa riba zata cigaba da zuwa,” a cewar Dangote.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng