An canza wa wata Mata hanci a Ingila

An canza wa wata Mata hanci a Ingila

Da sanadin kafar watsa labarai ta BBC Hausa mun samu rahoton cewa, a yayin da wata cuta da ake kira ANCA Positive Vasculutis, ta addabi wata mata a kasar Ingila, Jayne Hardman, ta sanya an sauya mata karan hanci da kofofinsa.

Wannan cuta da aturanci a kuma ilimin kimiya ake kira da ANCA Positive Vasculutis, ta sanya hancin Mrs Hardman ya burma har kuma ya nane.

Sai dai da yake ilimin kimiya tare da fasahar zamani na tafiya hannu da hannu da juna musamman a wannan karni, burin matar ya cika yayin da aka kirkiro mata hantunan roba da za ta iya ci gaba da rayuwa da shi.

Kalli bidiyon matar da muka samo a shafin Youtube:

Rahotanni sun bayyana bayyana cewa, an hada hancin robar ne tare da mayen karfe saboda koda ya goce.

Likitoci sun bankado wannan muguwar cuta dake jikin uwar 'ya'ya biyun wadda ta fito daga yankin Redditch, Worcestershire a kasar Ingila, a yayin da wani karenta ya tumbuke mata karan hanci da ya sanya ya burma ciki.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel