Da duminsa: Shugaba Buhari ya tashi zuwa kasar Japan
Labarin da Legit.ng ta samu da yammacin ranar Lahadi daga shafin mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, na nuni da cewa shugan kasa, Muhammadu Buhari, ya tashi zuwa kasar Japan.
A cikin sanarwar da Bashir ya fitar, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Yokohama na kasar Japan domin wani halartar wani taron kasa da kasa da za a yi a ranar Laraba, 28 ga watan Agusta, 2019.
Za a yi taron ne a kan cigaban kasashen Afrika (CITAD), kuma wannan shine karo na bakwai da aka taba gudanar da taron tun da aka fara yinsa.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da takwaransa na jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrazak Abdulrahman, na daga cikin 'yan rakiyar shugaba Buhari zuwa taron na TICAD7.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng