In da ran ka: Kabilu 10 da mata suka fi maza daraja

In da ran ka: Kabilu 10 da mata suka fi maza daraja

Mutane da dama zasu yi mamakin cewa akwai wasu kabilu a duniya da mata ne ke jan ragamar al'amura. A irin wadannan kabilu, mata sun fi maza muhimmanci.

Ga wasu daga cikin irin kabilun duniya da bincike ya gano cewa mata sun fi maza muhimmanci:

1. Kabilar Mosuo a kasar China: Kabilar Mosuo da wasu ke kira 'Na' karamar kabila ce a kasar China da ke da yawan mutanen da aka yi kiyasin cewa zasu kai 40,000.

A kabilar Mosuo, mata ne ke gudanar da aiyukan rike iyali kamar gudanar da sana'o'i da aikin gona da kuma kula da daukan dawainiyar yaran da suka haifa da mazansu.

Ana matukar girmama mace a kabilar Mosuo saboda irin hidimar da suke yi wajen rike iyali. Maza basu da wani aiki takamaimai a kabilar Mosuo, domin koda karfin mace ya kare ta fuskar daukar nauyin iyalinta, sai dai danginta su taimaka mata.

Mata ne ke zabar mazan da suke so, kuma sai dai mijin yake ziyartar matar da ta aure shi. Mace na da ikon ta auri namiji fiye da daya a kabilar Mosuo.

2. Kabilar Minangkabau a kasar Malaysia: Ita ce kabila mafi girma a duniya da mata keda matukar iko da muhimmanci fiye da maza. Adadin mutanen kabilar Minangkabau ya kai miliyan 4.2.

A duniyar kabilar Minangkabau, mata ne ke yin mulki kuma diya mace ce kadai zata iya gadon mulki ko kayan da mahaifiya ta mutu ta bari.

Harkokin addini ne kadai maza ke jagoranta a kabilar Minangkabau.

Mace za ta cigaba da zama a gidan iyayenta koda kuwa ta yi aure, sai dai mijin da ta aura yake kawo mata ziyara, kuma mace ce keda ikon zabin mijin da take son aura.

Sai dai, gabatar da shari'ar Musulunci a yankin da kabilar Minangkabau ke rayuwa ya fara rage karfin ikon da mata keda shi a kabilar.

3. Kabilar Akan a kasar Ghana: Ana samun 'yan kabilar Akan ne a yankin kudancin kasar Ghana. Mata ne ke yin komai a kabilar Akan - daga batun salsala, gadon kadara, zuwa samun damar hawa kujerar mulki koda kuwa ta siyasa ce.

Namiji kan iya samun mulki a kabilar Akan idan ya gada daga wurin mahaifiyarsa, a hakan ma sai idan 'yan uwansa mata sun hakura, kuma idan ya hau mulkin dole yake dama wa da iyalin 'yan uwansa mata.

4. Kabilar Bribri a kasar Costa Rica: Karamar kabila ce da ake samu a tsaunikan yankin 'Caribbean coastal' na kasar Costa Rica da arewacin Panama.

Mata na da matukar muhimmanci a kabilar Bribri, saboda hatta gadon kadarori 'ya'ya mata ne kawai ke samu.

Aikin da maza ke yi a kabilar Bribri shine gyara gawa idan an yi mutuwa, rera waka yayin binne mamaci da kuma dafa abincin da masu jana'iza zasu ci.

5. Kabilar Garos a kasar Indiya da yankin kasar Bangladesh: Ana samu 'yan kabilar Garos a jihohin Meghalaya, Assam, Tripura, Nagaland a kasar Indiya da kuma wasu sassan kasar Bangladesh.

Duk da maza ne ke yin mulki a kabilar Garos, mata ne kawai ke mallakar kadarori tare cin moriyar gadon mahifiya idan ta mutu.

A kabilar Garos, ana dauke yaro daga gaban iyayensa da zarar ya balaga tare da mayar da shi kauye, inda zai je ya zauna ya karbi horo a gidan gwagware, kuma ko bayan aure, namiji ne ke tare wa a gidan mace.,

Sai dai, zuwan zamani ya canja al'amura a kabilar Garos. Yanzu maza da mata na samun gadon iyayensu kuma 'ya'ya maza da mata na samun kulawa ba tare da nuna banbanci ba.

Ragowar su ne:

6). Kabilar Nagovisi da ke kudancin Bougainville, wani tsibiri da ke yammacin 'New Guinea'.

7). Kabilar Serer da ke kasar Gambia da kudancin kasar Mauritania.

8). Kabilar Aawambo ko Ovambo a kasar Namibia.

9). Kabilar Nubians da ake samu yanzu a kasar Sudan kudancin kasar Misa (Egypt).

10). Kabilar Ngazidja da ke Comoros.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel