Dan Allah nan gaba indai za aje yiwa wani dan siyasar Najeriya duka a kirani zan bayar da gudummawa - Dan gidan Fela Kuti

Dan Allah nan gaba indai za aje yiwa wani dan siyasar Najeriya duka a kirani zan bayar da gudummawa - Dan gidan Fela Kuti

- Dan gidan fitaccen mawakin nan marigayi Fela Kuti ya bayyana cewa idan har wata kungiya ta shirya dukan wani dan siyasa a kasar waje ba a sanar dashi ba to be yafe ba

- Seun ya bayyana cewa yana yankin Turai a lokacin da aka daki tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu, amma ba a gayyace shi ba

- Seun Kuti mutum ne kamar mahaifinsa da yake da tsattsauran ra'ayi akan gwamnatin Najeriya

Seun Kuti ya roki 'yan kungiyar 'yan aware na Biafra da kuma sauran kungiyoyi da su taimaka su sanar da shi a duk lokacin da suka shirya ciwa wani dan siyasa mutunci a kasar waje.

A cewar shi, yana yankin Turai a lokacin da aka kaiwa Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, hari a kasar Jamus ranar 17 ga watan Agustan nan.

Kamar dai yadda mahaifinsa yake, Fela Anikulapo Kuti, Seun shima yana da tsattsauran ra'ayi akan yanayin gwamnatin Najeriya.

KU KARANTA: Allah ya saka da alkhairi: Hadiza Gabon na sake ginawa tsohon da ruwan sama ya rushewa gida a jihar Yobe

Da yake hira da manema labarai a wata tattaunawa da suka yi, Seun ya ce:

"Abinda zan ce shine nan gaba idan wata kungiya ta shirya cin zarafi, ko dukan wani dan siyasa a kasar nan, kuma basu sanar da ni ba to ban yafe ba.

"Wannan shine kawai abinda zance akan wannan maganar, saboda ina yankin Turai nima a zaune, ayi mini magana a duk lokacin da za a daki wani dan siyasa ina da gudummawar da zan bayar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel