'Yan siyasa 20 da suka fi sa'o'insu kudi a duniya
Babu shakka arziki kashi ne kuma tako shi ake kamar yadda Hausawa suka bayyana, hakan ta kasance a yayin da muka kawo muku jerin manyan attajiran 'yan siyasa na duniya guda 20 da suka yi wa sa'o'insu zarra ta fuskar tarin dukiya.
Wannan kididdiga kamar yadda shafin yanar gizo na Wealthy Gorilla ya bayyana, ya ce ya kalato ta ne daga mujallar nan ta duniya mai fidda kididdiga a kan al'amuran da ke wakana a ban kasa.
Ga dai jerin hamshakan attajiran 'yan siyasa guda 20 da suka fi sa'o'insu kudi a shekarar nan da muke ciki ta 2019: Mun kawo muku wannan jerin attajirai daki-daki, sunayensu, mukamai, da kuma arzikin da suka mallaka.
20. Donald Trump - Shugaban Kasar Amurka
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 3.1
19. Hans-Adam II - Yariman Liechtenstein
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 3.5
18. Ross Perot - Hamshakin dan kasuwa na jam'iyyar Independent Party da yayi takarar shugabancin kasar Amurka a shekarar 1992 da kuma 1996.
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 3.5
17. Yarima Haji Abdul Azim - Magajin Sarkin Brunei; Sultan Haji Hassanal Bolkiah
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 5
16. Kim Jong-Un - Shugaban kasar Koriya ta Arewa
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 5
15. Imelda Marcos - 'Yar siyasa kuma jakadan kasar Phillipines - Tsohuwar matar tsohon shugaban kasar Phillipines, Ferdinand Marcos
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 5
14. Sultan bin Mohammed Bin Saud Al Kabeer - Yarima kasar Saudiya, kuma da na 12 ga Sarki Abdulaziz
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 6
13. Abdulla bin Ahmad Al Ghurair - Hamshakin dan kasuwa a Hadaddiyar Daular Larabawa wanda ya kasance dangin Al Ghurair a birnin Dubai.
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 6
12. Abdul Aziz Al Ghurair - Hamshakin dan kasuwa a Hadaddiyar Daular Larabawa wanda ya assasa bankin Mashreq a birnin Dubai.
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 7.5
11. Silvio Berlusconi - Tsohon Firaiministan Italiya kuma mamallakin kungiyar kwallon kafa ta AC Milan
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 8.5
10. Muhammad bin Salman - Yariman Saudiya
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 10
9. Mohammed Hussein Al Amoudi - Hamshakin dan kasuwa a kasar Habasha
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 12.6
8. Shaikh Mohammed bin Rashid al Maktoum - Firaiministan Hadaddiyar Daular Larabawa kuma Sarkin Dubai
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 14
KARANTA KUMA: 'Yan kasuwar Kano sun nemi Buhari ya tsige shugaban hukumar Kwastam, Hameed Ali
7. Sheikh Khalifa Bin Zayed Nahyan - Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa kuma Sarkin Abu Dhabi
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 18
6. Sultan Hassanai Bolkiah Mu’izzaddin Waddaulah - Sarki Kasar Brunei
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 20
5. Alwaleed Bin Talal Alsaud - Yariman Saudiya
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 20
4. Sheikh Mansour bin Zayed Al Nahyan - Firaiministan Hadaddiyar Daular Larabawa
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 30
3. Maha Vajiralongkorn - Yariman kasar Thailand
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 30
2. Michael Bloomberg - Dan siyasa a kasar Amurka kuma tsohon Magajin garin birnin New York
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 56
1. Vladmir Putin - Shugaban Kasar Rasha
Arziki: Dalar Amurka Biliyan 70
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng