Kasar Indiya: Babu sunan mutum miliyan 2 a cikin jerin ‘Yan Garin Assam

Kasar Indiya: Babu sunan mutum miliyan 2 a cikin jerin ‘Yan Garin Assam

Kusan mutane miliyan biyu ne su ka nemi sunayensu, su ka rasa a sabon rajistar Mazauna jihar Assam da ke Arewa maso Gabashin kasar Indiya. Hakan na nufin mutanen na iya rasa mafaka.

An fitar da jerin Mazauna jihar ne a Ranar Asabar, 31 ga Watan Satumba, 2019, bayan kusan shekara guda kenan gwamnatin jihar Assam ta na wannan aiki. Sunayen yana dauke da mutane miliyan 31.1.

Akwai mutane miliyan 1.9 da ba a sa sunansu a cikin sabuwar rajisatar ba. Rahotanni daga Aljazeerah sun bayyana cewa mafi yawan wadanda ba su ga sunansu ba, Musulmai ne da ke zama a jihar.

Gwamnatin jihar ta Assam ta na ikirarin cewa ta bi a hankali yadda ya dace wajen wannan aiki. Jawabin da gwamnatin ta yi, ya nuna cewa babu wanda aka toyewa hakki lokacin da ake tattara sunayen.

Hukumomin na kasar Indiya sun ce sun yi wannan aiki ne domin su gano Bakin da su ka shigo kasar a boye daga Bangladesh mai makwabtaka da ita. Tun 1971 mutanen Bangladesh su ke ci-rani a Indiya.

KU KARANTA: Mutanen Neja su na so Gwamnatin Najeriya ta sulhunta wani tsohon rikici

An cire sunayen wadanda su ka zo kasar bayan 1971 daga jerin. Wasu na ganin an shirya wannan ne don korar Musulmai daga kasar ta Indiya. Al’ummar Musulmai su ne daya bisa ukun mutanen da ke kasar.

A karshen makon jiya ne mutane su ka rika cinrindo domin duba sunayensu. Wani Manomi mai suna Mijanur Rahman ya ga sunansa da na ‘Ya ‘yansa uku amma babu sunan matarsa da wasu ‘Ya ‘yansa mata.

Wannan mataki da gwamnati ta dauka ya tadawa Mazauna wannan yanki hankali. Wadanda aka cire sunayensu su na da wa’adin watanni hudu domin su tabbatarwa hukuma cewa su ainihin ‘Yan kasa ne.

Babban Ministan Garin Assam, Sarbananda Sonowal, ya yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu. Sarbananda Sonowal yace za su dauki matakin da ya dace ga wadanda ba su ga sunayensu ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel