Kome yayi zafi haka: Wata mata ta kashe 'Ya'yanta guda biyu sannan ta kashe kanta

Kome yayi zafi haka: Wata mata ta kashe 'Ya'yanta guda biyu sannan ta kashe kanta

- Rahotanni sun bayyana cewa wata mata dake zaune a kasar Amurka ta kashe 'ya'yanta guda biyu sannan ta kashe kanta

- Wannan lamari ya biyo baya ne jim kadan bayan ta wallafa wani rubutu a shafinta na Instagram game da 'ya'yan nata

- Matar tayi amfani da bindiga ne ta harbesu duka, inda ta kuma juya bakin bindigar zuwa kanta ta harbe kanta ita ma

Wata mata dake zaune a birnin Georgia dake kasar Amurka an ruwaito cewa ta kashe 'ya'yanta guda biyu sannan ta juya bakin bindigar da tayi amfani da ita wajen kashesu ta kashe kanta.

A cewar rahoton, matar mai suna Marsha Edwards ta harbe 'ya'yan nata guda biyu mace da namiji, jim kadan bayan ta hau shafin yanar gizo tayi magana akan su.

Matar ta wallafa wani rubutu a shafinta na Instagram inda ta ce: "ba zan iya neman yara wadanda suka fi wadannan ba," wannan rubutu ya fito ne awanni kadan kafin a gano gawarta ranar Larabar nan da ta gabata.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Mujallar fim ta kalubalanci Rahama Sadau da amfani da mazaunan roba a wani hoto da ta dauka

'Ya'yan nata Erin Edwards mai shekaru 20 a duniya da kuma Christopher Edwards Jr. mai shekaru 24 a duniya, duka an ruwaito mutuwarsu sanadiyyar harbin da mahaifiyarsu ta yi musu.

An bayyana cewa daga uwar har 'ya'yan duka 'yan kungiyar 'yan jarida ne ta 'National Association of Black Journalists.'

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel