Hotunan dawowar Shugaba Buhari gida daga taron kasar Japan
Labari ya iso mana dazu nan cewa shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya dawo gida daga taron da ya halarta a kasar Jafan. An yi wannan taro ne daga Ramar 28 zuwa 30 na Watan Agusta.
Jirgin shugaban Najeriyar ya taba kasa ne da kimanin karfe 11:37 na daren Asabar. Wani daga cikin Hadiman shugaban kasar, Bashir Ahmaad, ne ya nuna bidiyon dawowar shugaban kasar.
Buhari ya iso Najeriya ne ta babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Garin Abuja, tare da ‘Yan tawagarsa da wadanda su ka take masa baya zuwa Garin Yokohama na kasar ta Jafan.
Gwamnonin da aka yi tafiyar da su; Babagana Zulum, Abdulrahman AbdulRazaq da kuma Babajide Sanwo-Olu duk sun shigo gida lafiya tare da sauran manyan jami’an gwamnatin kasar.
KU KARANTA: An saki mutanen Arewa da aka cafke a Legas su na ci-rani
A wajen wannan taro da aka shirya a kasar ta Asiya, shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a madadin Najeriya a wani zama da aka yi, sannan kuma ya gana da wani Sarki a Birnin Tokyo.
Bayan nan, shugaban na Najeriya ya yi amfani da wannan dama har ya gana da manyan ‘yan kasuwan kasar wajen domin ganin sun zo Najeriya sun buda kamfanoni da za su kawo abin yi.
Manyan Jami’ai da hafsoshi sun fito sun tarbi shugaban kasar a filin jirgi. Tun a karshen makon jiya ne shugaba Buhari ya bar Najeriya domin wannan taro. A 2016 an taba yin shigensa a Kenya.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng