Buhari bai damu da kisan kiyashi da ake yi wa 'yan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu ba - Reno Omokri
Shahararren dan adawar nan wanda ya ke yi wa kansa kirari da "Mai Azabtar da Buhari" "Buhari Tormentor", Mr. Reno Omokri, ya bayyana ra'ayin sa da cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari bai da wata damuwa dangane da kisan kiyashi da ake yi wa 'yan Najeriya m kasar Afirka ta Kudu.
Sanannan dan adawar nan na shugaban kasa Buhari, ya bayyana hakan ne a shafin sada zumunta na Twitter kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Omokri wanda ya wallafa takaitaccen tarihin tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, ya kira shugaban kasa Buhari da sunan "Janar", tare da cewa babu abinda ya shallin shugaban kasar da kisan gilla da ake yi wa 'yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu domin mafiya akasarin su sun kasance 'yan kabilar Ibo wato Inyamurai a yaren Hausa.
Ga sakon da Reno Omokri ya wallafa a shafinsa na Twitter
Biyo bayan ci gaba da kai farmaki da munanan hare-hare na kin jinin al'ummar Najeriya da kuma harkokin kasuwancin su a kasar Afirka ta Kudu, wasu daga cikin al'ummar kasar nan sun nemi da a kauracewa duk wata harkar cinikayya ta makociyar kasar.
Musamman mazauna babban birnin kasar nan na tarayya wato Abuja, 'yan Najeriya da dama yayin ganawa da manema labarai na jaridar Daily Trust, sun bayyana ra'ayoyin su kan dakile duk wata harkar cinikayya da kasar Afirka ta Kudu, lamarin da suka ce wata dangartaka ta zumunci da ke tsakanin kasashen biyu ta yanke a yanzu.
A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, gwamnatin tarayya ta zayyana wasu matakai da zata dauka domin kawo karshen hare-haren da ake kai wa 'yan Najeriya da wuraren kasuwancinsu a kasar Afrika ta Kudu.
KARANTA KUMA: Wani Mahaifi ya kashe dan sa da ya saci N500 a Akwa Ibom
Ministan harkokin kasashen ketare, Mista Geoffrey Onyeama, ne ya bayyana hakan ranar Talata bayan kammala wani taron hadin gwiwa da babban jakadan kasar Afrika ta Kudu a Najeriya, Mista Bobby Moroe.
A cewar ministan, daga cikin matakan da gwamnatin Najeriya ta dauka akwai batun hadin gwiwa a tsakanin jami'an tsaron kasashen biyu, lamarin da Ministan ya ce zai bai wa jami'an tsaron Najeriya da ke ofishin jakadanci Najeriya a kasar Afrika ta Kudu damar aiki tare da takwarorinsu na kasar domin bayar da kariya ga 'yan Najeriya da dukiyoyinsu.
Kazalika, gwamnatin Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta fara biyan diyya ga dukkan 'yan Najeriya da hare-haren ya shafa.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng