Kasashen Duniya
Rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da Isra'ila ya shafe kwana bakwai ana yi lamarin da ya samo asali daga harin da Isra’ila ta kai wanda Iran ta mayar da martani.
A labarin nan, za a ji cewa kasar Iran ta bayyana cewa ba za ta amince da hawa teburin tattaunawa da duk wadanda ke goyon bayan Isra'ila ta kai mata hari ba.
Shugaban China, Xi Jinping ya ce Iran sun saba da gwagwarmaya tun shekaru da dama da suka wuce. China ta kawo hanyoyi hudu domin kawo karshen fadan.
Bayan hare-haren da Isra’ila ta kai cikin Iran, kawayenta sun yi gum, sai Rasha ce kaɗai ta tsaya da ita, yayin da CRINK ke kiran zaman sulhu a yankin.
Farmakin makami mai linzami daga Iran ya jawo rufe tashar jirgin ƙasa ta birnin Beersheba a ƙasar Isra'ila, harin ya taɓa cibiyar fasaha da sansanin soji.
A labarin nan, za a ji cewa kasar Iran ta tabbatar da cewa ba za ta sassuta a harin kare kai da ta ke kai wa Isra'ila ba har sai dakarun IDP sun dakata.
Iran ta kai farmaki kan babbar cibiyar kimiyya ta Weizmann a Isra’ila, ta lalata dakunan gwaje-gwaje, a matsayin ramuwar gayya kan kashe masananta.
Sanata Ben Murray-Bruce ya ce ya hango cewa ana daf da shiga yakin duniya na uku sakamakon mallakar makamin nukiliya. Ya ce Najeriya za ta zauna lafiya a yakin.
Jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya karanto ayar Kur'ani ya karfafi 'yan Iran su cigaba da fafatawa da Isra'ila. Ya ce idan akwai tsoro ba za a ci nasara ba.
Kasashen Duniya
Samu kari