Forbes: Dukiyar Marigayi Hosni Mubarak ba ta kai Dala Biliyan 700 ba

Forbes: Dukiyar Marigayi Hosni Mubarak ba ta kai Dala Biliyan 700 ba

A shekarar 2011 aka fitar da wani rahoto da ke bayani game da tulin dukiyar da shugaban kasar Masar na lokacin watau Hosni Mubarak ya mallaka a Duniya.

Mujallar Forbes ta ce ana hasashen cewa kudin da Hosni Mubarak ya ba baya sun kai Dala biliyan 70. Sai dai wasu na ganin cewa kudin Mobarak ya wuce haka.

Jaridun kasar waje irinsu The Guardian da kuma ABC News sun kiyasta cewa dukiyar shugaban na Masar wanda ya yi shekaru 30 a kan mulki ya haura Biliyan $700.

A cewar wadannan Jaridu, Hosni Mubarak ya tada kai da fiye da Dala biliyan 700. Sai dai Forbes ta bayyana cewa an zuzuta dukiyar dadadden shugaban kasar.

Mubarak ya yi mulki a kasar Masar daga shekarar 1981 zuwa 2011, inda ake zargin cewa ya tara makudan kudi. Ko da dai jama’a su kan zuzuta irin arzikin na sa.

KU KARANTA: Za mau karbe jiragen Attajiran da bashi ya yi masu katutu a Najeriya

Forbes: Dukiyar Marigayi Hosni Mubarak ba ta kai Dala Biliyan 700 ba
Ana zuzuta dukiyar Marigayi Hosni Mubarak da ya yi shekarau 30 ya na mulki
Asali: UGC

Idan ta tabbata cewa Mubarak ya mallaki fam biliyan 70, to da ya zama na biyu a jerin Attajiran Duniya a shekarar 2011 – Zai zama ya sha gaban Bill Gates.

Binciken da Forbes ta yi ya nuna cewa Sarkin Kasar Thailand kuma Sultan din Brunei da Sarkin Saudi (na wancan lokaci) duk ba su mallaki Dala biliyan 70.

Forbes ta kan fitar da sunayen masu kudin Duniya amma ba ta ambatar da shugabannin kasashe domin ya na wahala a iya gane adadin dukiyar da su ka mallaka.

A cewar Mujallar Washington Post akwai yiwuwar Gidan Mubarak sun yi gaba da abin da ya kai Dala biliyan 700 na kudi da kayan alatu irinsu gwal da sauransu.

Washington Post ta ce daga cikin dukiyar da Iyalin Hosni Mubarak su ka yi awon gaba da su akwai tarin gwal-gwalai da ke hannun babban bankin kasar Amurka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel