Babbar matsalar mu a yau ita ce rashin tsaro – Gbajabiamila ya fadawa Sin

Babbar matsalar mu a yau ita ce rashin tsaro – Gbajabiamila ya fadawa Sin

Yayin da rashin tsaro ya ke cigaba da dabaibaye Najeriya, shugaban majalisar wakilan kasar ya na cigaba da neman gudumuwa da taimakon kasashen ketare.

Mai girma Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya roki kasar Sin watau China ta kawowa gwamnatin Najeriya agaji domin ta magance matsalolin da kasar ke ciki.

Shugaban majalisar wakilan tarayyar ya gabatar da kokon bararsa ne a lokacin da ya karbi bakuncin Jakadar kasar ta Sin a Najeriya, Mista Zhou Pingjian.

Femi Gbajabiamila ya nemi alfarma wajen kasar Sin ta hannun Jakadanta, inda ya shaida masa da cewa rashin tsaro ne babbar matsalar Najeriya a halin yanzu.

Honarabul Gbajabiamila ya ce: “Babbar matsalar mu a halin yanzu ita ce matsalar rashin tsaro, kuma za mu yi murna mu samu taimako yanzu daga gare ku.”

KU KARANTA: Boko Haram Gbajabiamila ya tunatar da Amurka game da jiragen yaki

Babbar matsalar mu a yau ita ce rashin tsaro – Gbajabiamila ya fadawa Sin
Shugaban Najeriya Buhari da Tawagarsa wajen wani taro a Sin
Asali: Depositphotos

Kakakin majalisar wakilan ya shaidawa Zhou Pingjian cewa gwamnatin Najeriya za ta yi farin-ciki da kowane irin taimako ta samu daga kasarsa a halin da ake ciki.

Ya ce: “Za mu yi murna da samun taimako da kowace irin hanya za ku iya. A kan maganar huldar tsaro, za mu yi farin cikin samun taimako daga gare ku (kasar China)”

Jaridar Daily Trust ta ce Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi wannan rokon alfarma ne a Ranar Talata, 18 ga Watan Fubrairun 2020 lokacin da ya hadu da Jakadan.

Jakadan na Sin a Najeriya ya sha alwashin cewa kasarsa za ta cigaba da kokari wajen ganin ta taimakawa Najeriya cin ma bukatunta kamar yadda Jaridar ta rahoto.

Idan ba ku manta ba, kwanaki shugaban majalisar ya yi irin wannan ganawa da Jakadar Amurka a babban birnin tarayya Abuja, ya kuma mika kokon barar Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel