Gwajin coronavirus: Shugaban kasar Amurka Donald Trump bai dauke da cuta

Gwajin coronavirus: Shugaban kasar Amurka Donald Trump bai dauke da cuta

Shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump ya yi gwaji domin gano ko cewa ya na dauke da cutar nan ta Coronavirus da ta zama annoba yanzu a kasashen Duniya.

Kamar yadda labari ya zo mana daga gidan jaridar New York Times, sakamakon wannan gwaji da shugaban na Amurka ya yi, ya nuna cewa bai dauke da cutar.

Fox News sun fitar da wannan rahoto ne a Ranar Asabar, 14 ga Watan Maris, 2020. Ana sa ran ba da dadewa ba, Duniya za ta san halin da Donald Trump ya ke ciki.

Tun a baya a lokacin da ya gana da Manema labaran da ke cikin fadar shugaban kasa, Mai girma Donald Trump ya shaida masu cewa garau ya ke jin kansa.

Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa jikinsa bai yi wani zafi ba. Zafin jiki da tari su na cikin alamomin wannan cuta ta Coronavirus da ba a gane kanta ba.

KU KARANTA: Fitacciyar Jarumar Kannywood Ladi mutu-ka-raba ta mutu

Coronavirus: Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi gwaji
Donald Trump ya yi gwajin Coronavirus bayan ya hadu da Wajngarten
Asali: Twitter

Donald Trump ya yi gwajin ne a sakamakon haduwar da ya yi da Tawagar shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro, da wasu manyan jami’an gwamnatinsa a makon jiya.

Babban Sakataren yada labarai na gwamnatin Jair Bolsonaro watau Fabio Wajngarten ya na cikin wadanda su ka hadu da Trump, kuma yanzu haka ya na dauke da cutar.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan shugaban kasar ya nemi mutanensa su komawa Ubangiji game da wannan mummunar cuta da ta kashe mutane 5, 000 a Duniya.

Idan ba ku manta ba dai, kasar Mexico ta fara tunanin rufe iyakokinta da kasar Amurka a dalilin wannan cuta. Mexico ta na ganin hakan zai rage yaduwar annobar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng