Darajar kudin Najeriya: Kasashe 8 da takardun Naira za su mayar da mutum tamkar Sarki

Darajar kudin Najeriya: Kasashe 8 da takardun Naira za su mayar da mutum tamkar Sarki

Da yawan 'yan Najeriya kan dauka cewa sai mutum ya mallaki wasu makudan kudi sannan zai iya daukan dawainiyar fita wasa kasa. Amma ba haka abin yake ba, domin kuwa akwai wasu tsirarun kasashe da takardun kudin Najeriya keda matukar daraja, kuma idan ya mallake su zai samu daukaka a irin wadannan kasashen.

1. Kasar Uganda

Uganda kasa ce da ke gabashin nahiyar Afrika. a kasar Uganda, Naira daya ta Najeriya daidai take da 'Shillings' 10.15 na kasar (1 NGN = 10.15UGX).

Duk da rayuwa tana da 'yar tsada a kasar Uganda, abinci da nau'in kayan sha suna da sauki, watau akwai araha.

2. Kasar Cambodia

Tsuburin Ankorwat ya kara daukaka sunan Cambodia a duniya. Kimanin mutum miliyan 40 ke ziyartar kasar kowacce shekara da sunan yawon bude ido.

Tattalin arzikin kasar ya dogara ne a kan sarrafa atamfa. Naira daya daidai take da 11.24 'Riel' na kasar Cambodia.

3. Vietnam

Addinin 'Buddhism' ake yi a kasar Vietnam, wacce ta balle daga kasar China bayan an fafata yaki. Vietnam ce a mataki na 13 a cikin kashen da suka fi yin suna a duniya.

N1 = 64.26 VND, watau Naira daya ta Najeriya daidai take da 64.26 na kudin kasar Vietmam.

Darajar kudin Najeriya: Kasashe 8 da takardun Naira za su mayar da mutum tamkar Sarki
Kudin Najeriya
Asali: UGC

4. Malagasy

Malgas wani muhalli ne a wani tsibiri ne da ke dama da tekun 'Breede' a yammacin Cape. Muhallin yana da nisan kilomita 25 daga arewa maso yammacin tekun 'Breede' da nisan kilomita 30 daga kud maso gabashin Swellendam.

N1 = 10.14 Malagasu Ariary, watau Naira daya ta Najeriya daidai take da 10.14 na kudin kasar Malagasy.

5. Kasar Indonesia

Jama'a na yawan ziyartar manya da kananan tsaunika da ake yi wa lakabi da 13466 a kasar. Mutum ba zai kashe wani kudi masu yawa ba saboda Naira daya ta Najeriya daidai take da 40.03IDR na kudin kasar Indonesia.

DUBA WANNAN: Ibrahim Ibrahim: Dan Najeriya da aka yanke wa hukuncin kisa a kasar Saudiyya ya samu 'yanci

6. Kasar Sao Tome

Masu son kwalam da makulashe zasu ji dadin ziyartar kasar Sao Tome domin yawon bude ido. Suna da abubuwa masu kayatar wa kamar su fulawoyi, fadar masarautu da sauransu.

N1 = 59.36 STD, watau Naira daya ta Najeriya daidai take da 59.36 na kasar Sao Tome.

7. Kasar Mongolia

Kasar Mongolia, mai makwabtaka da China da Russia, ta yi suna saboda al'adarsu ta kiwon dabbobi.

Naira daya ta Najeriya daidai take da Turic 7.64 na kasar Mongolia (N1 = 7.64 Turic).

8. Kasar Paraguay

Paraguay kasa ce marar fadin kasa da ke tsakanin kasashen Argentina, Brazil da Bolivia. Zuwa kasar Paraguay ba zai gigita tattalin arzikin mutum ba saboda Naira daya ta Najeriya daidai take da 'Guarani' 17.99 na kasar Paraguay (N1 = 17.99 Guarani).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel