Watakila Amurka ta kawo mana Coronavirus – Gwamnatin Kasar China

Watakila Amurka ta kawo mana Coronavirus – Gwamnatin Kasar China

Mai magana da yawun bakin ma’aikatar harkokin kasar waje na kasar Sin, ya nuna cewa watakila Dakarun Amurka ne su ka shigo da cutar Coronavirus cikin Garin Wuhan.

Kalaman ma’aikatar kasar wajen ya kara hura wutar rikici tsakanin kasar da kuma Amurka. Kasar Sin ta yi wannan magana ne bayan Amurka ta zarge ta da sakaci kwanaki.

Amurka ta bakin Robert O’Brien ta bayyana cewa ta na ganin cewa kasar ta Sin ba ta dauki matakin da ya dace cikin gaggawa domin takaita aukuwar wannan anonoba ba.

Mai ba shugaban kasar Amurka shawara a kan harkar tsaro, Robert O’Brien, ya nuna cewa hukumomin Sin sun rika boyewa jama'a gaskiyar lamarin wannan muguwar cuta.

Zhao Lijian wanda ya ke magana a madadin ma’aikatan waje na kasar Sin ya yi jawabi a shafinsa na Tuwita, ya na maidawa Amurka martani da cewa ita ce ta ke boye gaskiya.

KU KARANTA: Donald Trump ya yi gwajin cutar Coronavirus, an gano halin da ya ke ciki

Watakila Amurka ta kawo mana Coronavirus – Gwamnatin Kasar China

Kasar China da Amurka su na zargin juna a kan boye gaskiyar annobar Coronavirus
Source: Twitter

Lijian ya ce: “Yaushe aka fara samun cutar a Amurka? Mutum nawa su ka kamu da cutar? Ina sunan asibitocin? Watakila sojojin Amurka ne su ka kawo cutar cikin Wuhan.”

Mista Zhao Lijian ya karasa da fadawa Amurka cewa: “Ku rika yin abubuwa ke-ke-da-ke-ke. Ku fito ku bayyana alkalumanku. Mu na bin Kasar Amurka bashin karin bayanai.”

Duk da wannan bayani da Zhao Lijian ya yi a Tuwita, bai fito ya fadi hujjojin da ke gaskata zargin da ya ke yi na cewa Sojojin Amurka su ka shigo da wannan cuta cikin Sin ba.

Wannan cuta da ta bayyana a Garin Wuhan da ke kasar Sin ta kashe fiye da mutane 5000 a Duniya daga karshen bara zuwa yanzu. Kasashen su na ta maidawa juna raddi,

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel