Karfin tattalin arzikin mu ya yi kasa – Inji Gwamnatin Najeriya

Karfin tattalin arzikin mu ya yi kasa – Inji Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta fito ta koka da halin da tattalin arzikin kasar ya shiga a halin yanzu. Ministan kwadago, Chris Ngige, shi ne ya koka a makon nan.

Dr. Chris Ngige ya ce karfin tattalin arzikin kasar ya durkushe, inda ya alakanta wannan matsala da dogaro da gwamnatin tarayya ta yi a kan arzikin mai.

A cewar Ministar, abubuwa ba su tafiya daidai yadda ya kamata a kasar. Najeriya mai mutane kusan miliyan 200 sun dogara ne kaco-kam da man fetur.

Chris Ngige ya yi wannan jawabi ne a Ranar Talata, 18 ga Watan Fubrairun 2020 lokacin da ya gana da Jakadar kasar Amurka a Najeriya a Garin Abuja.

Da ya ke magana da Jakada Mary Beth Leonard a babban birnin tarayya Abuja, Minista Ngige ya shaida mata cewa karfin tattalin arzikin Najeruya ya yi kasa.

KU KARANTA: Diezani-Madukwe saci Biliyan 800 daga dukiyar Najeriya– Inji EFCC

Karfin tattalin arzikin mu ya yi kasa – Inji Gwamnatin Najeriya
Ngige ya ce dogara da man fetur ya sa Najeriya a matsala
Asali: Facebook

“Karfin tattalinmu ya yi kasa; mun san mun yi kuskuren dogara da arzikin mai.” Ngige ya nuna cewa tsagerun Neja-Delta sun bada gudumuwar karya tattalin.

“Lokacin da farashin mai ya gangaro kasa, aka samu matsalar tsageranci wanda ya rage yawan hako mai Neja-Delta, abin da mu ke samu ya yi kasa sosai.”

Haka zalika dazu nan mu ka samu labari cewa hukumar bada lamuni ta Duniya IMF ta rage burin da ta ci a kan Najeriya game da motsawar tattalin arzikin kasar.

A baya IMF ta na sa rai tattalin Najeriya zai habaka da 2.5% a shekarar 2020. Yanzu hukumar ta dawo ta tafi da hasashen bunkasar tattalin arziki na 2.0% a bana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel