Tirkashi: Wani mutumi da ya mutu ya tashi yayin da ake kokarin sanya shi a kabari
- Wani matashin saurayi da likita ya bayar da sanarwar cewa ya mutu ya tashi a lokacin da ake shirin binne shi
- Saurayin dan kasar Indiya ya hadu da hatsarin mota, sai aka yi gaggawar garzayawa dashi asibiti domin ceto rayuwar shi
- To sai dai bayan karfin 'yan uwanshi ya kare basu da kudin magani sai likita ya kawo musu shi gida ya ce musu ai ya mutu, bayan kuma bai mutu ba
An riga an gama tona kabari, iyalan mamacin sun gama hallara, ana shirin sanya gawar a kabari, amma sai wani abin mamaki ya faru, inda gawar ta tashi, lamarin da ya faru a kasar India.
Mutanen da suke ta faman jimamin mutuwar Mohammed Furqan sun cika da mamaki a yayin da wanda suke ganin su da sake haduwa dashi sai dai ko a lahira, bayan likita ya sanar musu da cewa ya mutu ba zai dawo ba, sai gashi yana da rai bai mutu ba.
Cikin gaggawa aka nufi asibiti da matashin saurayin dan shekara 20 a duniya domin ceto rayuwarshi.
Amma labarin wannan sha da kyar da wannan saurayi a birnin Lucknow ya bawa kowa mamaki a kasar, hakan ya sanya aka fara tambaya akan ingancin ma’aikatar lafiya a kasar, tilas ya sanya aka fara bincike a jihar ta Uttar Pradesh.
Tun lokacin da Furqan ya hadu da hatsari a ranar 21 ga watan Yunin shekarar 2019, an bayyana cewa ya mutu a ranar Litinin, bayan dangin shi sun bayyana wani asibitin kudi na kasar da suka danka amanar kula da lafiyarshi sun bayyana musu cewa ya mutu saboda basu da kudin biyan kudin magani.
An dawo dashi gida a cikin motar asibiti a ranar tare da likita da yake bayyana cewa ai ya riga ya mutu.
KU KARANTA: Dan takarar shugaban kasar Amurka ya zabi Musulmi ya shugabanci yakin neman zaben shi
Yayan Furqan mai suna Mohammed Irfan, ya ce sun shiga cikin damuwa da rudewa akan wannan maganar.
Ya bayyanawa jaridar Hindustan Times: “Muna shirin binne shi sai wasu daga cikin mu suka ga yana motsi. Cikin gaggawa muka dauke shi zuwa asibitin Ram Manohar Lohia, inda likita ya bayyana mana cewa yana raye, aka saka masa abin numfashi domin ceto ranshi.
“Mun biya asibitin kudin da muka fara kai shi kimanin naira miliyan hudu (N4m), amma da muka sanar musu da cewa karfin mu ya kare, sai kawai suka ce mana ai Furqan ya mutu.’
Narendra Agarwal, shugaban ma’aikatan lafiya na Lucknow, ya ce: “Mun fara bincike akan lamarin, kuma zamu dauki kwakkwaran mataki a kai.”
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng