Guinea-Bissau: Cipriano Cassamá ya sauka daga kujeran Shugaban rikon-kwarya

Guinea-Bissau: Cipriano Cassamá ya sauka daga kujeran Shugaban rikon-kwarya

Cipriano Cassamá ya sauka daga kujerar shugaban kasar Guinea-Bissau bayan kwana guda a kan mulki, a dalilin barazanar da rayuwarsa ta rika fuskanta.

Idan ba ku manta ba, rikici ya kaure a Guinea-Bissau wanda hakan ya sa ‘Yan majalisa su ka zabi Cipriano Cassamá a matsayin sabon shugaban rikon kwarya.

‘Yan majalisar G/Bissau sun nada Cipriano Cassamá a kan kujerar shugaban kasa ne sakamakon ja-in-jar zaben da aka samu, har sai kotun koli ta yanke hukunci.

Cassamá ya dare kan mulki ne a daidai lokacin da tsohon Sojan kasar da ya shiga siyasa ya kuma lashe zaben bara, Umaro Cissoko Embaló, ya rantsar da kan sa.

Kasar ta shiga halin dar-dar a ‘yan kwanakin nan inda Jami’an tsaro su ke ba Ministoci da masu rike da mukamai kariya daga barazanar juyin mulkin gwamnati.

KU KARANTA: An rantsar da Umaro Embolo a matsayin Shugaban G/Bissau

Guinea-Bissau: Cipriano Cassamá ya sauka daga kujeran Shugaban rikon-kwarya
Cassamá ya sauka daga mulki sakamakon barazanar kashe shi
Asali: Depositphotos

Jaridar The Nation ta Najeriya ta ce a halin da ake ciki yanzu a kasar Afrikan, manyan Sojoji ne ke gadin gidan daya daga cikin masu ikirarin Firayim Minista a kasar.

A daidai kusa da gidan Firayim Minista Aristides Gomes, akwai gidajen Ministocin shari’a, tattalin arziki, da kiwon kifi, da su ke karkashin kulawar Dakarun Soji.

Jaridar ta ce duk da wannan dar-dar da masu mulki su ka shiga, sauran Bayin Allah su na cigaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da nuna wani jin tsoro ba.

A zaben 2019, Umaro Embaló ya doke Simoes Pereira amma gwamnatin kasar ta tafi kotu, ta ce an yi magudi a wannan zabe da jam’iyyar hamayya ta yi nasara.

Tsohon shugaban kasa José Mário Vaz ya mika mulki ga Embaló. Amma kuma ‘Yan majalisa sun rantsar da Cassamá ne a matsayin shugaban kasan wucin-gadi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel