Gwamnatin Amurka ta baiwa Masallatai daman kirar Sallah ta lasifika

Gwamnatin Amurka ta baiwa Masallatai daman kirar Sallah ta lasifika

A karon farko, Musulman kasar Amurka sun samu daman kirar Sallah a bayyane ta hanyar amfani da na’aurar lasifika, watau amsa kuwwa, ba kamar yadda suka saba yi a baya a asirce a baya ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamnatin birnin Peterson na jahar New Jersey ne suka bayar da wannan dama ga Musulmai mazauna yankin, tare da sanya hakan cikin dokokin su, ta yadda kiran Sallah a lasifika ba zai taba zama laifi ba.

KU KARANTA: Gwamnatin Kano za ta dauki matasa 2,200 don aikin samar da tsaro

A karkashin sabon kudurin dokar, za’a cire kiran Sallah daga cikin hayaniya dake damun jama’a, kuma za’a baiwa Masallatai daman kirar Sallah daga karfe 6 na safe zuwa karfe 10 na dare a kowanne rana.

A yanzu dai akwai sauran taron jin ra’ayin jama’a guda biyu da za’a gudanar a kan wannan kudurin doka kafin a fara aiwatar da shi, amma zuwa yanzu ya samu amincewar mahukunta a birnin Peterson, inda a cikin mutum 9, mutane 7 sun amince da shi.

Wata kungiyar addinin Musulunci dake kasar Amurka, Council of American Islamic Relations, reshen jahar New Jersey, CAIR, ta yi maraba da wannan doka tare da bayyana farin cikinta game da shi.

A cewar CAIR: “Mun jinjina ma mahukuntan Peterson na daukan wannan mataki mai kyau da zai kara hada kan jama’a, kuma muna basu kwarin gwiwar su tabbatar da kudurin ya zama doka.

“Wannan doka ta nuna damuwar hukuma ga mutunta addininmu, kuma hakan ya tabbatar da yadda suke ganin girman addinai mabambanta a wannan yankin.” Inji CAIR.

A nan gida Najeriya kuwa, gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jahar Kano ta kammala shirin daukan sabbin jami’an tsaro guda 2,200 domin taimaka ma hukumomin tsaro dake jahar wajen samar da ingantaccen tsaro.

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Abba Anwar a ranar Alhamis, wanda ya bayyana cewa za’a dauki matasan ne daga kananan hukumomin jahar 44, inda kowacce karamar hukumar za ta samu jami’ai 50.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel