Harin ta’addanci a Masallaci ya jikkata Musulmi 1 a kasar Faransa
Wani dan bindiga shi daya tilo ya bude ma masallata wuta a wani masallaci dake birnin Paris na kasar Faransa, inda ya yi harbin mai kan uwa da wabi, wanda ya yi sanadiyyar jikkatar mutum daya.
Jaridar Mirror ta ruwaito da misalin karfe 8 na daren Lahadi ne dan bindigan ya kaddamar da harin, inda ya yi harbe harbe da dama a harabar Masallacin dake titin Rue de Tanger 19 arrondisment.
KU KARANTA: Majalisar dokokin jahar Kaduna ta yi dokar rage talauci a tsakanin talakawan Kaduna
A dalilin harbin mai kan uwa da wabin ne dan bindigan ya dirka ma wani musulmi da ya je Masallacin da nufin gabatar da sallah, harsashi har sau biyu a kafa, kuma nan take ya fice daga cikin Masallacin, ya hau kan titi, inda ya tsere a kan keken-babur.
Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito tuni an garzaya da mutumin da harin ya shafa, wani matashi dan shekara 32, zuwa asibitin Pitie-Salpetriere. Rahotanni sun tabbatar da akwai mutane 15 a cikin masallacin a lokacin harin.
Koda Yansanda suka isa, sun tarar da kwankon harsashi samfurin 9mm a harabar Masallacin.
Idan za’a tuna a kwanakin baya ma an samu kwatankwacin wannan harin a birnin Landan na kasar Birtaniya, inda wani dan ta’adda ya caka ma ladanin Masallaci wuka a wuya, da kyar aka ceto rayuwarsa.
Shi dai wannan dan ta’adda ya kasance yana yawan halartar sallah a wannan masallaci kamar yadda masallata suka tabbatar, a wannan rana yana tsaye ne a bayan ladanin, kammala tayar da Iqamarsa keda wuya sai ya caka ma ladanin wuka.
Amma Yansanda sun samu nasarar kama shi, sai dai zuwa yanzu basu gabatar da shi gaban kotu don fuskantar hukuncin da ya dace da shi ba sakamakon suna ci gaba da gudanar da bincike a kansa.
A hannu guda kuma, shi kuwa ladanin da harin ya rutsa da shi, dattijo mai shekaru 71 a duniya ya bayyana cewa tuni ya yafe ma maharin nasa, domin kuwa a cewarsa yafiya na daga cikin koyarwar addinin Musulunci.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng