Umaro Embalo ya rantsar da kansa a matsayin Shugaban Guinea-Bissau

Umaro Embalo ya rantsar da kansa a matsayin Shugaban Guinea-Bissau

A jiya Ranar Alhamis, 27 ga Watan Fubrairun 2020, Mista Umaro Sissoco Embalo, ya rantsar da kanshi a matsayin sabon shugaban kasar Guinea-Bissau.

Kamar yadda mu ka samu labari daga rahoton AFP, Umaro Sissoco Embalo, ya yi rantsuwar hawa kan kujerar shugaban kasa, a sakamakon zaben da ya lashe.

Idan ba ku manta ba, Umaro Sissoco Embalo shi ne ‘Dan takarar da ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi a kasar Guinea-Bissau a karshen shekarar bara.

Shugaban kasar mai ci, wanda ya sha kashi a zaben watau Domingos Simoes Pereira, bai amince da zaben ba, tuni ya kuma shigar da kara a babban kotun koli.

Sai dai Sissoco Embalo ya watsi da halin da ake ciki, inda ya ratsar da kan shi a matsayin sabon shugaban kasa, dinbin mutane sun halarci wannan rantsuwa jiya.

KU KARANTA: Cutar Coronovirus ta shigo Najeriya ta hannun wani Bature

Umaro Embalo ya rantsar da kansa a matsayin Shugaban Guinea-Bissau
Lokacin da Umaro Sissoco Embalo ya ziyarci Shugaba Buhari
Asali: UGC

‘Dan siyasar ya ratsar da kan shi ne a wani babban otel da ke kasar ta Afrika ta Yamma. Umaro Sissoco Embalo ya yi alkawarin cewa zai yi aiki da dokar kasa.

“Na rantse zan kare kundin tsarin mulki, zan bi dokar kasa sau da kafa, kuma zan girmama ta.” Inji Jagoran hamayyar Guinea-Bissau a babban birnin Bissau.

An yi wannan taro ne duk da rikita-rikitar da ake fama da ita a gaban kotu da kuma turka-turkar siyasar da kasar Afrikan ta shiga a sakamakon zaben na 2019.

Ba wannan ba ne karon farko da shugabannin Afrika su ka ki sauka daga kan mulki. A dalilin irin haka kasashen Afrika su kan barke da rikicin da ke cin al’umma.

A Najeriya an yi irin wannan a shekarun baya, inda Marigayi MKO Abiola ya gabatar da kan sa a matsayin shugaban kasa, a dalilin haka aka daure shi a kurkuku.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel