Jihar Kaduna
Wasu tsagerun 'yan bindigan daji sun sheƙe manoma uku, sun tattara wasu manoman da matafiya da ke kan hanyar zuwa kasuwa a Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya nada tsohon kwamishinan tsaron cikin gida na Nasir El-Rufai, Samuel Aruwan A matsayin shugaban Hukumar Kula da Birane (KCTA).
'Yan bindiga a dajin Kagarko da ke jihar Kaduna sun harbe kafar wani da ya yi kokarin guduwa daga komarsu mai suna Ifeanyi a karamar hukumar Kagara ta jihar.
Mutane sun shiga damuwa da tashin hankali bayan da aka wayi garin ranar Asabar da labarin tsintar wani jariri a kusa kango da ba a kammala ba a birnin Kaduna.
Wasu miyagun mahara sun halaka babban basaraken Fulani da ke a wani ƙauye a ƙaramar hukumar Zaria cikin jihar Kaduna. Maharan sun kuma halaka ƴaƴansa guda huɗu.
Magidanci a jihar Kaduna ya kai ƙarar tsohuwar matarsa gaban kotun shari'ar musulunci saboda ƙin bar masa. Ya koka cewa har dukan tsiya ƴan uwanta suka yi masa.
Ƴan bindiga sun halaka wasu manoma biyu a ƙauyen Unguwar Gajere cikin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a wani sabon hari da suka kai zuwa yankin.
Ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar ƙaramar hukumar Chikun, ya riga mu gidan gaskiya kwana huɗu bayan an rantsar da su. Ya rasu bayan rashin lafiya.
Hukumar kula da abinci da magunguna ta NAFDAC ta kai samame tare da kulle kamfanin hada magungunan gargajiya na Baban Aisha da ke Tafa cikin birnin Kaduna.
Jihar Kaduna
Samu kari