Kaduna: NAFDAC Ta Yi Dirar Mikiya A Kamfanin Hada Magungunan Gargajiya Na Babban Aisha, Ta Rufe Kamfanin

Kaduna: NAFDAC Ta Yi Dirar Mikiya A Kamfanin Hada Magungunan Gargajiya Na Babban Aisha, Ta Rufe Kamfanin

  • Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta NAFDAC ta kai samame kamfanin hada magungunan gargajiya a jihar Kaduna
  • Hukumar ta ce ta samu kamfanin da gaza bin ka'idar hada magungunan gargajiya wanda ya sabawa doka
  • Hukumar ta ce lasisin kamfanin na Baban Aisha ya bar aiki tun a shekarar 2018 yayin da mai kamfanin ya zo sabunta shi

Jihar Kaduna - Hukumar kula da abinci da magunguna ta NAFDAC ta kai samame kamfanin hada magungunan gargajiya na Baban Aisha da ke Kaduna.

Kamfanin hada magungunan gargajiyan da ke Tafa kan hanyar Kaduna zuwa Abuja an rufe shi ne sakamakon samun korafi daga wasu mutane a yankin.

NAFDAC ta rufe kamfanin hada maganin gargajiya a Kaduna
Irin Magungunan da Kamfanin Ke Hadawa. Hoto: Premium Times.
Asali: Facebook

Umar Sulaiman shugaban bangaren bincike na hukumar ya ce wannan rangadi suna yi ne don kiyaye lafiyar al'umma, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Sai Na Ga Bayanku: Sabon Gwamnan APC a Arewa Ya Yi Babban Tanadin Karar Da ’Yan Bindiga

Umar ya ce hukumar ta fita ran gadi ne da kuma rufe kamfanin

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun fita rangadi da kai samame kamfanin magungunan gargajiya mai suna Sacramultilink mallakin Dakta Salisu Sani wanda aka fi sani da Baban Aisha.
"Mun taru anan ne don abu daya, shi ne kare lafiyar al'umma, wannan kamfani ya saba ka'idojin hada magani da kuma lasisi wanda ya dade da barin aiki.
"Sannan an karya ka'idar hada magungunan gargajiya wanda basu da rijista da hukumar NAFDAC da kuma rashin tsafta wurin hada su, wannan shi ne dalili."

Ya kara da cewa:

"Zamu rufe wannan kamfani da kuma kama duk wani ma'aikaci da yake nan, wannan kamfani ya yi rijista don hada magani daya ne kacal, tun daga ranar bamu sake ganin shi ba.
"Ya yi gaban kanshi wurin kara hada magungunan gargajiya daban-daban, wannan ya sabawa doka kuma ba haka tsarin aiki ya ke ba."

Kara karanta wannan

Yadda El-Rufai Ya Nemi a Soke Kotun Shari’a da Gargajiya Inji Tsohon Shugaban Majalisa

Shugaban hukumar a jihar ya bayyana dalilin rufe kamfanin

Shugaban hukumar reshen jihar Kaduna, Nasiru Mato ya ce lasisin kamfanin ya bar aiki tun 2018, yayin mai kamfanin ya zo don sabunta shi, cewar rahotanni.

Yayin da hukumar ta bashi wasu takardu don cikawa wanda ka'ida ce kafin kamfani ya samu amincewa daga hukumar don ci gaba da gudanar da ayyukansa.

NAFDAC Ta Yi Gargadi Game da Wani Magani Mai Kisa, Ta Tura Sakwanni Ta Imel

A wani labarin, Hukumar NAFDAC ta gargadi mutane kan wani mai kisa da ke jawo cututtuka.

Babbar daraktar hukumar, Mojisola Adeyeye ne ta bayyana haka a ranar Laraba 26 ga watan Afrilu.

Daraktar ta ce maganin na tari ne kuma yana da hatsarin gaske ga lafiyar al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel