Jihar Kano
Kwamitin karbar mulki na zababben gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya zargi Gwamna Ganduje da yi wa shirinsu kafar ungulu don ganin ba a karbi mulki lafiya ba.
Ganduje ya biya tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafen jama'a ta jihar, Rimin Gado hakkokinsa na sama da naira miliyan 5 a kotu.
Wani matashi ya shiga hannu bayan da ya kwace wayar wata mata da kuma kokarin soka mata wuka a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma. Ya bayyanayadda ya yi satar.
Wata babbar kotun jihar Kano ta amince da bukatar wani tsohon alkalin majistare na neman a tilastawa Atoni Janar na jihar gurfanar da Doguwa kan zargin kisa.
Mutuwa rigar kowa, Rijistaran jami'an Bayero University Kano watau BUK, Malam Jamilu Ahmad Salim, ya rigamu gidan gaskiya ranar Laraba 26 ga watan Afrilu, 2023.
Yanzu muke samun labarin cewa, Allah ya yiwa tsohon ministan Najeriya na kwadago rasuwa bayan da ya yi jinya a wani asbitin jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.
Wani abin bakin ciki ya faru a karamar hukumar Madobi ta Jihar Kano yayin da wani jirgin ruwa ya yi hadari kuma an kasa rayyuka 5 amma an ceto mutane shida.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nemi zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya taimaka ya ƙarisa ayyukan da lokaci ba zai bari ya kammala su ba.
Gwamna Abdullahi Ganduje, ya ce shi baya gaba da kowa yayin da zai bar kujerar mulki, yana mai bukatar magajinsa da ya kammala ayyukan da gwamnatinsa ta fara.
Jihar Kano
Samu kari