Abba Gida-Gida Zai Sake Duba Batun Tsige Tsohon Sarkin Kano Sanusi, Inji Kwankwaso

Abba Gida-Gida Zai Sake Duba Batun Tsige Tsohon Sarkin Kano Sanusi, Inji Kwankwaso

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, gyara da yiwa masarautun Kano garambawul na hannun sabon gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Kwankwaso ya ce, an raba masarautun Kano gida biyar, amma akwai bukatar a duba tare ad kawo mafitar da ta dace
  • Idan baku manta ba, an tsige sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II a shekarar 2020 tare da korarsa ya bar Kano gaba daya

Jihar Kano - Dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce gwamnatin Kano mai jiran gado za ta sake duba batun tsige Alhaji Muhammadu Sanusi daga sarautar Kano.

Sanusi dai ya zama sarkin Kano ne a lokacin mulkin Kwankwaso, inda daga baya gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tsige shi.

An tsige Sanusi daga kujerarsa ne a ranar 9 ga watan Maris din 2020, kana aka yi masa ature zuwa garin Loko, wani kauye mai nisan gaskiya a jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Shehu Sani ya tona asirin Buhari, ya fadi gaskiyar dalilin dage kidaya

Kwankwaso ya fadi matsayar Abba Gida-Gida kan masarautar Kano
Abba Gida-Gida da Kwankwaso | Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Hakazalika, Ganduje ya kuma rarraba masarautun jihar Kano, inda ya nada sabbin sarakuna masu iko daya guda biyar a manyan masarautun jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abba Gida-Gida zai sake duba batun tsige Sanusi

Da yake magana a cikin wani bidiyo, Kwankwaso ya ce, gwamnatin Abba Kabir Yusuf da za ta fara a ranar 29 ga watan Mayu za ta sake duba batun tsige Sanusi.

Da yake magana game da lamarin masarautar Kano, Kwankwaso ya ce:

“Mun yi kokari ba mu sanar da maganar sarki - ko za a cire ko za a sa ko za a yi kaza ba, amma yanzu ka ga dama ta samu, su wadanda Allah ya bai wa wannan ragama su za su zauna... Za su je su duba su gani mene ne ya kamata su yi a halin da suka samu kansu.”

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Kogi: Shugaba Buhari Ya Yarda Ododo Ya Gaji Yahaya Bello

Da yake tsokaci game da batun Sanusi da batun karkasa masarautun Kano, Kwankwaso ya ce:

“Ita sarautar yanzu an kasa ta kashi biyar, duka wadannan da aka yi dole sai an zo an yi nazari.
“Mun tabbatar shi wannan gwamna Allah zai ba shi hikima da basira na yadda zai zo ya warware wadannan matsaloli da aka zo aka shuka a Jihar Kano.”

A bangare guda, Ganduje ya ce a shirye yake ya mika mulkin Kano ya Abba Gida-Gida cikin aminci ba tare da wata matsala ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel