Jihar Kano
Kwamishinan 'yan sanda a jihar Kano, Hussaini Gumel ya umarci kama sifetan 'yan sanda da ya hallaka matashi a jihar yayin da ake zanga-zangar hukuncin kotu.
Sabon shugaban ma'aikatan jihar Kano, Musa Abdullahi ya gargadi ma'aikatan jihar da su guji zuwa wurin aiki a latti inda ya kafa musu lokacin zuwa aiki.
Dan majalisar mazabar Tudun Wada/Doguwa ya zargi jam'iyyar NNPP ta tafka magudi a zaben gwamnan jihar da ya gudana a 2023. Ya ce NNPP ta yi amfani da kuri'un bogi.
Rahoton nan yana tattare da matsaya da jan hankali a kan hukunce-hukuncen kotuna a shari’ar Abba Kabir Yusuf da APC daga bakin Sen Kawu Sumaila OFR.
Kungiyar Progressive League of Youth Voters (PLYV) ta bayyana cewa akwai wani shiri da ake yi na tayar da hargitsi a garin Kano a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba.
Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bode George, a martanin da ya yi kan tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya ce akwai kuskure alkalai suɓsoke zabe.
Allah ya yi wa diyar Sarkin Kano Ado Bayero rasuwa a safiyar ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba. Hauwa Lele, kanwa ce ga sarkin Kano na yanzu da kuma sarkin Bichi.
Babbar kotun jihar Kano ta sanya ranar 6 ga watan Disamba na wannan shekara a matsayin ranar yanke hukunci kan shari'ar dan China saboda kisan budurwarsa, Ummita.
Tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kotun Daukaka Kara ta yi na ci gaba da haifar da tashin hankali a jihar Kano, yan sanda sun kama masu shirin tayar da tarzoma 7.
Jihar Kano
Samu kari