Inyamurai Igbo
Doyin Okupe ya nemi afuwan 'yan Najeriya kan bautunsa na bai wa Ibo shugabancin Najeriya a zaben 2023. Ya bayyana nadama sosai tare da neman afuwar a yafe masa.
Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta ce yankin ta jajire don ganin hadin kai da ci gaban kasar, sai dai kuma ta ce tana son a dunga adalci da daidaito wajen yin komai.
Kungiyar dattawan arewa da yawun shugabanta, Ango Abdullahi, tayi zargin cewa yan kabilar Igbo ne ƙashin bayan duk wata ta'asa da ake yiwa yan Arewa a kudu.
Kungiyar dake goyon bayan Igbo suyi shugabancin kasa ta (IPSC), ta ware mutane 11 daga yankin Kudu maso Yamma da ake sa ran zasu fito takarar shugabancin kasa..
Soyayya na da dadi amma idan aka hadu da wanda ake so nagari. Aishat Ugochi Obi da Nurudeen (Nicholas) Iekocha wadanda suka koma Musulunci a jihar Imo zasu yi aure. Za a yi gagarumin auren ne a ranar 10 ga watan Afirilun 2020...
Dattijon Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa akwai yiwuwar jama’an kabilar Ibo su samu mulkin Najeriya amma fa sai sun kulla kyakkyawar alaka da sauran yankunan kasar, musamman Arewa.
Hadaddiyar kungiyar kabilar Inyamuran Najeriya ta nanata manufarta na ganin yankin kabilar Ibo, kudu masu gabashin Najeriya ta fitar da shugaban kasa a zaben shekarar 2023, kamar yadda shugabanta, Nnia Nwodo ya bayyana.
Kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo ta babbatar ma yan Najeriya cewa ayyukan kungiyar masu fafutukar neman yan Biyafara wanda aka fi sani da IPOB zai zo karashe ne idan kasar ta tsayar da dan Igbo a matsayin shugaban kasa a 2023.
Kungiyar Musulman Inyamuran Najeriya tace tun da Najeriya ta zama kasa guda ba su taba karuwa ba. Kungiyar ta SEMON nemi Shugaba Buhari ya rika nada wadanda su ka cancanta a mukaman Gwamnati kuma ya guji kabilanci.
Inyamurai Igbo
Samu kari