2023: Babban Fasto ya yi hasashen wanda zai karbi shugabanci daga hannun Buhari

2023: Babban Fasto ya yi hasashen wanda zai karbi shugabanci daga hannun Buhari

  • Shararren fasto na Najeriya, Prophet Elijah Moses, ya yi hasashen cewa dan kabilar Igbo kuma kirista ne zai karbi mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
  • Prophet Elijah ya kuma ce Allah ya nuna masa cewa 'yan kabilar ne za su mamaye gwamnati a dukkan matakai ciki harda majalisar dokokin tarayya
  • Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulki za ta sha mummunan kaye a zabe mai zuwa

Jihar Imo - Yayin da babban zaben 2023 ke kara gabatowa, babban limamin coci a Najeriya, Prophet Elijah Moses, ya yi hasashen cewa kabilar Igbo za ta samar da shugaban kasa.

Faston ya kuma bayyana cewa Allah ya nuna masa gagarumin kaye da ke jiran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a zaben, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Read also

APC da PDP ba za su taba sauyawa ba: Jega ya bayyana matsalolin APC da PDP

2023: Babban Fasto ya yi hasashen wanda zai karbi shugabanci daga hannun Buhari
2023: Babban Fasto ya yi hasashen wanda zai karbi shugabanci daga hannun Buhari Hoto: Femi Adesina
Source: Facebook

Sai dai kuma, Elijah, wanda ya fito daga yankin Umuneke, Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo, ya yi ikirarin cewa bai san wacce jam’iyyar siyasa bace za ta samar da shugaban kasar.

Da yake jawabi ga manema labarai a Owerri a ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba, Faston ya ce:

“Allah ya nuna mani cewa ‘yan kabilar Igbo kuma kiristoci za su mamaye gwamnati a dukkan matakai, ciki harda majalisar dokokin tarayya sannan kuma dan Igbo kirista zai karbi shugabancin kasar nan a 2023 kuma zai kawo ci gaba sosai a kasar nan.”

2023: Jonathan zai dawo a matsayin shugaban kasa, Shahararren Fasto ya yi hasashe, ya bada sharadin cikar haka

A baya mun kawo cewa wani babban fasto na cocin Abuja, The Resurrected Assembly (GROM), Prize F. Aluko, ya yi hasashen cewa Goodluck Ebele Jonathan zai dawo a matsayin shugaban kasa a 2023.

Read also

2023: Mun shirya tsaf don yin kaca-kaca da APC a Zamfara, mataimakin gwamna

Fasto Aluko a cikin hasashensa na baya-bayan nan ya bayyana cewa Jonathan ya bar ofis a 2015 saboda akwai horo da Allah yake son yi masa kan wasu ayyuka da zai cimma a nan gaba, The Sun ta ruwaito.

Jagoran na GROM ya kara da cewa yanzu da Allah ya shirya tsohon shugaban kasar, lokaci ya yi da za a bi abin da Madaukakin Sarki ya nufa a kan shi, wanda shine shugabanci.

Source: Legit

Online view pixel