Mulkin Najeriya: Ku bar korafi, ku kulla kyakkyawar alaka da mutane – Tanko Yakasai ga kabilar Ibo

Mulkin Najeriya: Ku bar korafi, ku kulla kyakkyawar alaka da mutane – Tanko Yakasai ga kabilar Ibo

Dattijon Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa akwai yiwuwar jama’an kabilar Ibo su samu mulkin Najeriya amma fa sai sun kulla kyakkyawar alaka da sauran yankunan kasar, musamman Arewa.

Yakasai ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, inda yace: “Yan kabilar Ibo suna da daman samun shugaban kasa a Najeriya nan gaba kadan ko kuma a can gaba, a tsarin siyasar Najeriya ba’a samun mulki sai an hada kai da yankunan Arewa da kudu.

KU KARANTA: Duk shugaban da aka yi a Najeriya sai yan Najeriya sun zage shi, me yasa? – John Oyegun

“Dole ne sai inyamurai sun fara kokarin samun hadin kan sauran yankunan kasar musamman ma Arewa, ba wai kawai za su tsaya su yi ta korafi bane, kamata ya yi su fara kokarin kulla alaka da jama’a domin su bayyana manufofinsu, wannan abu ne mai yiwuwa.” Inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Inyamurai na daga cikin manyan kabilun Najeriya da suka mamaye yankin kudu maso gabashin Najeriya, amma sun gagara samar da shugaban kasa tun bayan dawowa mulkin dimukradiyya a shekarar 1999.

Wannan ne yasa yan kabilar Ibo suke ganin tamkar an mayar dasu saniyar ware a siyasar Najeriya. Tanko Yakasai ya bayyana wannan ra’ayi nasa ne bayan kwanaki 2 da cikar yakin basasan Najeriya shekaru 50, inda Najeriya ta yaki Inyamurai lokacin da suka yi kokarin ficewa daga kasar.

Da yake tsokaci game da yakin, Yakasai yace: “Akwai bambamce bambamce tsakanin Yakubu Gowon da Odumegwu Ojukwu, bana jin akwai wanda ya yi hasashen irin asarar da aka tafka a yakin, an kashe jama’a da dama daga kowanne bangare, babu wanda zai iya fadin iyakar asarar da aka yi.

A wani labarin kuma, tsohon shugaban jam’iyyar APC, Cif John Odigie Oyegun ya bayyana cewa tsarin mulkin dimukradiyya ya tabbata a Najeriya, tamkar takalmin kaza, mutu ka raba. Sai dai ya koka kan yadda yan Najeriya basa jin dadin tsarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel