Ga abunda yan Igbo ke so daga Nigeria, Ohanaeze ta bayyana

Ga abunda yan Igbo ke so daga Nigeria, Ohanaeze ta bayyana

- Mutanen Igbo na son hadin kan Najeriya kamar yadda babbar kungiyar yankin ta bayyana

- A cewar Ohanaeze, akwai bukatar yin adalci da nuna daidaito a komai

- Har ila yau, ta gargadi wadanda ke fafutukan samun wata kasa daga Najeriya kan kada su wuce iyakarsu

A wani lamari da zai zama kamar sauke nauyi ga yan Najeriya da dama, kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta ce yankin ta jajire don ganin hadin kai da ci gaban kasar.

Farfesa George Obiozor, Shugaban kungiyar ne ya bayyana hakan a yayin taronsa na maanema labarai, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya yi korafin cewa babu wani abu da zai kai ga rabe kasar Igbo daga sauran Najeriya.

Ga abunda yan Igbo ke so daga Nigeria, Ohanaeze ta bayyana
Ga abunda yan Igbo ke so daga Nigeria, Ohanaeze ta bayyana Hoto: Vanguard
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama mambobin hatsabibiyar kungiyar nan ta yan Shilla su 3 a Yola

Sai dai, ya ce kasar Igbo na son kasa inda ake adalci da daidaito a tsakanin al’umma.

Ya kuma ce ya zama dole a guji dukkan matakai da furucin da ke sanya mu a hanyar cutuwa.

A halin yanzu, ya yi kira ga Kanu da sauran masu fafutuka a kan kada su wuce iyakarsa.

Legit.ng ta kuma rahoto cewa sabon Shugaban kungiyar ta Igbo Ohanaeze Ndigbo ya bayyana cewa hakkin da aka rataya masu shine samar da Shugaban Najeriya dan Ibo a 2023.

Sabon zababben kakakin kungiyar, Alex Obonna ne ya bayyana hakan a lokacin hira da jaridar Daily Sun na ranar Asabar, 16 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar gwamnoni tayi martani yayinda Yahaya Bello yace kashe mutane ake so ayi da rigakafin korona

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba goyon bayan takarar shugabancin babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu ba.

An tattaro cewa mista Tinubu bai sanar da kudirinsa na takarar Shugaban kasa a 2023 ba a hukumance.

Sai dai kuma yayinda yake gabatar da jawabi a yayin rantsar da kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP a Dutse a ranar Laraba, Lamido ya ce Shugaban kasar ba zai cika alkawarin yarjejeniyar da suka kalla ta bangarensa ba, bayan ya samu goyon bayan shugabanni daga kudu maso yamma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel