Na yi nadama kwarai da gaske: Okupe ya nemi afuwa kan batun shugabanci Ibo

Na yi nadama kwarai da gaske: Okupe ya nemi afuwa kan batun shugabanci Ibo

- Doyin Okupe ya nemi afuwa daga 'yan kabilar Ibo da sauran 'yan Najeriya game da wata maganasa

- Doyin ya bayyana cewa, bai yi magana don cutarwa ga kabilar Ibo da 'yan Najeriya ba

- Ya bayyana manufar maganarsa da taimakawa don tabbatar da shugabancin Ibo a 2023

Doyin Okupe, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya nemi afuwa kan wasu maganganun da yayi a kan shugabancin Igbo a 2023.

Okupe, a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafin Twitter ranar Asabar, ya ce ta hanyar yarjejjeniyar kasa ne kadai dan kabilar Ibo zai iya zama shugaban kasa a 2023.

Tsohon hadimin ya kara da cewa irin wannan matsaya ba za ta iya fitowa ba har sai babbar yankin arewa ta yafe wa Ibo a kan juyin mulkin 1966 wanda ya kai ga kashe Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.

KU KARANTA: Bayan yin rigakafin Korona da kwana 2, Firaminista ya kamu da Korona

Na yi nadama kwarai da gaske: Okupe ya nemi afuwa kan batun shugabanci Ibo
Na yi nadama kwarai da gaske: Okupe ya nemi afuwa kan batun shugabanci Ibo Hoto: independent.ng
Source: UGC

"Yarjejeniyar kasa baki daya game da shugabancin Ibo ba za ta iya canzawa ba har sai yankin arewa ya yafe wa 'yan kabilar Ibo saboda kisan da sojojin Najeriya suka yi wa Sardaunan Sokoto da Ibo suka kitsa a juyin mulkin 1966," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Kalaman nasa ba su yi wa wasu 'yan Najeriya dadi ba, yayin da suka fara caccakarsa a kafofin sada zumunta na yanar gizo.

A yayin mayar da martani, Okupe, a ranar Asabar, ya yi amfani da shafinsa na Twitter don neman gafara ga Ibo da sauran ’yan Najeriya da suka ji haushin kalaman nasa kan shugabancin Ibo.

“Ina mika neman afuwata ga 'yan kabilar Ibo da sauran ‘yan Najeriya wadanda suka ji haushin maganata a kan shugabancin ibo da arewa.

"Ban yi niyyar cutarwa ko wulakanta Ibo ba. Madadin haka na so taimakawa ne don tabbatar da mafarkin. Na yi nadama game da sakon da na tura, kuma hakika ina neman afuwa,” in ji shi.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya na adawa da kashe sama da $1.5bn don gyaran matatar mai ta Fatakwal

A wani labarin daban, Wani dattijo dan kasa, Alhaji Bashir Othman Tofa, ya gargadi gwamnatin tarayya da kada ta yi biris da batun Gwamnatin Gargajiya ta Biyafara (BCG) da Alhaji Asari Dokubo, shugaban kungiyar Ceton Jama'ar Neja Delta (NDPSF) ya shelanta.

Alhaji Dokubo, wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban BCG ya kuma ce za a kafa tsarin larduna ga gwamnati; amma gwamnati, ta bakin Ministan Watsa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ta mayar da martani game da sanarwar inda ya bayyana ta a matsayin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel