Siyasa rigar yanci: Inyamurai sun lashi takobin shugabancin Najeriya a shekarar 2023
Hadaddiyar kungiyar kabilar Inyamuran Najeriya, Ohanaeze ta nanata manufarta na ganin yankin kabilar Ibo, kudu masu gabashin Najeriya ta fitar da shugaban kasa a zaben shekarar 2023, kamar yadda shugabanta, Nnia Nwodo ya bayyana.
Jaridar Guardian ta ruwaito Nwodo ya bayyana haka ne yayin kaddamar da littafin tarihin rayuwarsa a garin Nnewi, inda yace Inyamiri na da yancin zama shugaban kasa a Najeriya, kuma ba zasu lamunci duk wani kokarin dakile wannan yanci a zabe mai zuwa ba.
KU KARANTA: Yan fashi sun bindige babban Alkalin kotun shari’ar Musulunci, sun tasa keyar direbansa
Don haka Nwodo ya tubure a kan lallai ya kamata a yi ma kabilar Ibo adalci, kuma a duba musu, domin a cewarsa ya kamata a ce magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito daga yankin Ibo a shekarar 2023.
“Wannan Dimukradiyya ne, mutane na da ikon fadan duk abin da suke so, amma babban abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda za’a tabbatar da adalci, babu wani mai karancin yanci a Najeriya, don haka 2023 lokacinmu ne.” Inji shi.
Idan za’a tuna, a kwanakin baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan siyasar Najeriya, musamman masu burin tsayawa takara ko wacce iri a zaben shekarar 2023 dasu kada su kuskura su sanya shi cikin sabgar siyasarsu.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata, 17 ga watan Disamba yayin da yake tarbar manyan baki da suka kai masa ziyara a fadar Aso Rock Villa domin taya shi murnar cika shekaru 77 a duniya.
Buhari ya nemi yan siyasa masu burin tsayawa takara a zaben 2023 da su kasance sun yi aiki tukuru wajen yakin neman zabe, domin kuwa a wannan karo ba zai sake bari a yi amfani da sunansa wajen tafka magudin zabe ba.
Haka zalika shugaban kasa ya gargadi duk masu kokarin yin amfani da hukumomin tsaro da jami’ansu wajen gudanar da magudin zabe a zaben 2023 da cewa sun makara, kuma su sake tunani, domin ba zai taba bari su cika wannan buri nasu ba.
Don haka lokaci ne kadai zai tabbatar da kabilar Ibo za su iya darewa shugabancin Najeriya a zaben 2023, ko kuma shugaba Buhari zai mara ma bukatarsu baya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng